Daga Usman Mohammed Zaria

Gwamnatin jihar Jigawa ta sake jaddada kudirinta na cigaba da horas da matasa maza da mata sana’o’in hannu domin su kasance masu dogaro da kai.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan lokacin bikin yaye matasa 160 da suka sami horo akan sana’o’in dogaro da kai, wanda kungiyar hadin kai ta kafin Hausa ta gudanar.

Malam Umar Namadi ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta bullo da shirye-shirye da nufin mayar da matasan jihar masu dogaro da kawunansu.

A don haka, Gwamnan ya godewa Kungiyar bisa bada horan, tare da yin kira ga matasan da suka amfana da shirin su yi amfani da ilmin da suka samu domin zama masu dogaro da kai.

A jawabinsa na marhabun ,Shugaban Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa Alhaji Abdullahi Nalayi ya nuna farin cikinsa bisa kokarin kungiyar na shirya bada horan tare da bada tabbacin ci gaba da tallafawa matasan yankin domin zama masu dogaro da kai.

Shima a nasa jawabin shugaban kungiyar kafin Hausa Unity Forum Malam Abdullahi Suleiman yace an zabo matasan ne daga mazabu goma sha daya na yankin.

Kazalika, an raba kayayyakin bunkasa tattalin arziki ga matasan da suka hada da kekunan dinki da na’u’rorin dafa abinci masu amfani da wuta da kayayyakin yin tiles da kuma kwamfutocin tafi da gidan ka.

Sauran sun hada da kayayyakin yin takalmi da na dinki da na yin jaka da na yin biredi da kayayyakin sanya solar da dai sauran su.

Haka kuma Gwamna Umar Namadi ya kai ziyarar bazata wuraren aikin gina makarantar Tsangaya da kuma makarantar kere kere ta gwamnatin jihar.

Namadi ya bayyana gamsuwa da yadda ayyukan ke gudana, tare da bukatar  ‘yan kwangilar dake ayyukan da su kammala aikin akan lokaci kamar yadda aka tsara.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa masu dogaro da dogaro da kai

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

 

A nata tsokacin kuwa, kwamishiniya mai lura da ababen more rayuwa da makamashi a hukumar zartarwar kungiyar AU Lerato Dorothy Mataboge, kara tabbatar da alaka ta yi tsakanin hadin gwiwar Sin da Afirka, da burin da ake da shi na bunkasa masana’antu a sassan nahiyar.

 

Mataboge ta kara da cewa, yunkurin bunkasa samar da masana’antu a Afirka na bukatar karfafawa ta hanyar gina kwarewa, da horar da sana’o’i, da samar da cibiyoyi da albarkatun al’umma, don haka ta yi kira da a hada karfi-da-karfe wajen tsara shirye-shiryen bunkasa sanin makamar aiki a cikin gida, da samar da cibiyoyin horo masu nagarta, don horar da jama’a fasahohin amfani da makamashi marar gurbata yanayi. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi November 7, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil November 7, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo November 7, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura
  • Nigeria: Za A Ci Gaba Da Zaman Shari’ar Shugaban Kungiyar “IPOB” A ranar 20 Ga Watan Nan Na Nuwamba
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila
  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
  • An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
  • Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
  • Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki