Ajax ta kori kocinta John Heitinga
Published: 6th, November 2025 GMT
Kungiyar kwallon ƙafa ta Ajax da ke ƙasar Netherlands ta sanar da sallamar kocinta, John Heitinga, a sakamakon rashin kataɓus da a yanzu ƙungiyar ta maƙale a ƙasan teburin gasar Zakarun Turai ta Champions League.
A wata sanarwa da ta Ajax ta fitar a ranar Alhamis, ta ce tana neman sabon koci, inda a halin yanzu, Fred Grim zai riƙe aikin Heitinga har zuwa lokacin da za a naɗa sabon mai horarwa.
Heitinga, wanda ya sanya hannu kan kwantiragi na shekaru biyu a watan Mayu, ya gaza sauya akalar ƙungiyar, lamarin da Ajax ɗin ta tabbatar cewa ta kawo ƙarshen yarjejeniyar.
Daraktan fasaha na kulob ɗin, Alex Kroes, ya bayyana cewa wannan mataki “yana da raɗaɗi”, amma ya ce ya zama dole don ci gaban ƙungiyar.
“Mun san yana ɗaukar lokaci kafin sabon koci ya daidaita tawagar da aka yi mata zubin sabbin ‘yan wasa. Mun ba John wannan damar, amma yanzu mun ga ya dace mu naɗa wani sabon mutum,” in ji Kroes.
Mummunan sakamako na ƙarshe shi ne rashin nasarar da Ajax ɗin ta yi har gida a hannun Galatasaray a gasar Champions League, wadda ta doke ta 3-0 a ranar Laraba. Wannan na zuwa ne bayan da kwasar kashinta a hannun da ta yi yayin da Chelsea ta doke ta 5-1 a baya.
Haka kuma, Ajax ta sha kashi a hannun Marseille wadda ta doke ta 4-0, sai kuma ci 2-0 a hannun Inter Milan, lamarin da ya sa ta gaza samun ko da maki ɗaya a babbar gasar ta Turai.
A lig ɗin gida kuwa, Ajax tana matsayi na huɗu a teburin Eredivisie, da tazarar maki takwas tsakaninta da Feyenoord da PSV Eindhoven.
Magoya bayan kulob ɗin sun yi zanga-zangar rashin jin daɗi saboda yawan sauye-sauyen da Heitinga ke yi yayin wasanni, yayin da wasu ke ganin lokaci ya ƙure masa.
Sai dai ƙungiyar magoya bayan Ajax ta bayyana rashin jin daɗi bisa korar Heitinga, tana mai cewa: “Duk abin da muke so shi ne mu ga Ajax tana samun nasara, saboda haka rabuwa juna ba zai kai ga nasara ba.”
Heitinga dai tsohon ɗan wasan Ajax ne da ya buga wa ƙasarsa Netherlands wasanni 87.
Haka kuma, ya taɓa murza leda a Atletico Madrid, Everton da Fulham.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Genoa ta naɗa Daniele De Rossi sabon kociya
Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar. Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.”
Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League Ajax ta kori kocinta John HeitingaDe Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma.
Roma ce ƙungiyar da De Rossi ya kai zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar Europa League ta 2024, kafin a sallame shi bayan rashin nasara a wasanni hudu a jere a kakar da ta biyo baya.
A makon da ya gabata, Genoa ta kuma sallami daraktan wasanninta Marco Ottolini, inda ta maye gurbinsa da ɗan ƙasar Sifaniya, Diego Lopez.