Leadership News Hausa:
2025-11-08@20:14:15 GMT

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Published: 8th, November 2025 GMT

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa.

Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman mataki na uku da kuma wasan karshe.

 

Yadda aka raba rukunan gasar

An raba tawaga 24 da za ta buga gasar kofin Afirka zuwa rukuni shida dauke da hurhudu kowanne.

 

Rukunin A : Morocco, Mali, Zambia, Comoros. Rukunin B : Masar, Afirka ta Kudu, Angola, Zimbabwe

Rukunin C : NIjeriya, Tunisia, Uganda, Tanzania. Rukunin D : Senegal, Jamhuriyar Congo, Benin, Botswana. Rukunin E : Algeria, Burkina Faso, Ekuatorial Guinea, Sudan. Rukunin F : Ibory Coast, Kamaru, Gabon, Mozambikue

 

Kasashen da ake hasashen za su iya lashe gasar Morocco

Ita ce ta farko daga Afirka da ta kai zagayen daf da karshe a tarihi a Gasar Kofin Duniya da aka yi a Katar a 2022. Saboda haka tana sahun gaba da ake gannin za ta iya lashe kofin Afirka da take karbar bakunci. Rabon da kasar ta lashe kofin tun 1976, saboda za ta yi fatan daukar karo na biyu.

A gasar da aka yi a 2024, an yi waje da Morocco a zagaye na biyu wato ‘yan 16

Senegal

Mai rike da kofin 2022 za ta buga wasannin da kwarin gwiwa mai tarin fitattun ‘yan wasa da ke buga wasa a faɗin duniya karkashin Pape Thiaw, wanda ya maye gurbin Aliou Cissé. Senegal tana tare da tsoffin ‘yan wasanta da kuma matasan da suka hada da Sadio Mané da Kalidou Koulibaly da Edouard Mendy da Gana Gueye da Nicolas Jackson da Pape Matar Sarr da Habib Diarra da kuma Iliman Ndiaye.

Kawo yanzu Senegal ce kan gaba a yawan wasa ba tare da rahin nasara ba a duniya guda 25 sai Afirka ta Kudu da 23 da kuma Sifaniya mai wasa 22, Masar

Kasar Masar mai kofin Afirka bakwai tana cikin wadanda za su iya lashe kofin, wadda take karkashin Hossam Hassan ta yi wasa 12 a dukkan karawa ba tare da rashin nasara ba. Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Mohamed Salah yana daga fitattun ‘yan wasan tawagar da ake sa ran za su nuna kansa a wasannin.

 

Algeria

Mai koyar da tawagar ‘yan wasan kasar, Bladimir Petkobic yana ta kokarin ganin ya mayar da kasar kan ganiya, mai fitattun ‘yan wasa Mahrez da Slimani da kuma matasa Mohamed Amoura da Anis Hadj Moussa. Bayan da aka yi waje da Algeria karo biyu a jere bayan wasannin cikin

rukuni, kasar na fatan yin abin kirki a Morooco, kuma rabonta da kofin Afirka tun 2019.

 

Ibory Coast

Kasar Ibory Coast ce mai rike da kofin za ta yi kokarin sake lashe kofin karashin Emerse Faé. Duk da cewar ta yi rashin nasara a hannun Saliyo da Zambia, tawagar za ta Morocco da fitattun ‘yan wasa, illa dai akwai kalubale a matakin mai rike da kofin Afirka. Ibory Coast ce ta dauki kofin karo biyu daga gasar takwas a gasar cin kofin duniya daga cikin tawagogin da za su kece raini a Morocco.

 

Nijeriya

Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya wadda ta yi ta biyu a gasar da aka buga a Ibory Coast, za ta shiga wasannin da kwarin gwiwa. Super Eagles na da fitattun ‘yanwasa da suka hada da Bictor Osimhen da Lookman da Chukwueze da sauransu.

Yanzu dai hankali zai koma kan koci, Eric Chelle ko zai iya lashe kofin. Akwai Kasashen Da Ba a Saka su a lissafi saboda raunin tawagoginsu

 

Kamaru

A kodayaushe ba tabbas a Kamaru, bayan rashin jituwa tsakanin shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Samuel Eto da Marc Brys. Sai dai kasar ta yi wasanni 12 ba tare da rashin nasara ba, kodayake ta yi tuntube a hannun tsibirin Cape Berde. Kamaru wadda ta lashe kofin sau biyar tana da gogewa a wasannin gasar.

 

Jamhuriyar Congo

Ita ma jamhuriyar Congo za ta yi fatan daukar fansa a hannun Senegal, wadda ta doke ta 3-2 a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a badi. Ana sa ran tawagar wadda Yoane Wissa na Newcastle United da Fiston Mayele ke jan ragama, za ta so ta nunawa duniya cewar ba kanwar lasa ba ce.

 

Afirka ta Kudu

Bayan da Afirka ta Kudu ta taka rawar gani a wasannin da aka buga a 2023 da samun tikitin shiga gasar kofin duniya kai tsaye da za a yi a 2026. Afirka ta kudu na fatan nuna kwazo a wasannin da za ta fuskanta.

Kodayake yawancin ‘yan wasanta na buga wasa a gida daga Mamelodi Sundowns, duk da haka takan taka rawar gani da gagarar tawagogin da suke da fitattun ‘yan kwallon.

Za a buga gasar cin kofin Afirka a filaye tara cikin birane shida da suka hada da Rabat da Casablanca da Tangier da Agadir da Marrakech da kuma Fez. Birnin Rabat yana da manyan filaye hudu da suka hada da na Prince Moulay Abdellah Sports Compled, inda za a yi bikin bude gasar.

A Casablanca, filin Mohammed B da Wydad AC da Raja Casablanca ke wasanni, yana daga fitatcen filin da ake ji da shi a fadin kasar. Sauran biranen da za su karbi bakuncin wasannin sun hada da Tangier da Agadir da Marrakech da kuma Fez.

Jerin filayen da za a buga gasar

1 Prince Moulay Abdallah Sports Compled (Rabat)

2 Crown Prince Moulay El Hassan Sports Compled (Rabat)

3 El Barid Stadium (Rabat)

4 Olympic Anned Stadium of the Moulay Abdellah Compled (Rabat)

5 Mohammed B Stadium (Casablanca)

6 Fez Sports Compled (Fez)

7 Grand Stade de Tangier (Tangier)

8 Grand Stade de Marrakech (Marrakech)

9 Grand Stade d’Agadir (Agadir)

Me ya sa ‘Morocco ke kokarin mamaye kwallon kafar Afirka’a Getty

Kusan Shekaru 20 da suka wuce, Maroko ta rungumi wasanni, musamman kwallon kafa, ginshikin da tasirinta a Afirka da fiye da hakan. Ta hanyar karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka, tana da niyyar karfafa kimarta a matsayin kasa ta zamani mai kwanciyar hankali da kuma hangen nesa.

Nagartattun ababen more rayuwa na zamani ( filayen wasa da sufuri da otal-otal da dai sauransu) ba wai kawai alamar nasarar tattalin arziki ba da take da shi, tana kuma gudanar da mulki mai inganci da kishin nahiyar Afirka. Maroko na son gabatar da kanta a matsayin cibiyar kwallon kafa ta Afirka, mai iya shirya wani babban wasanni na kasa da kasa mai inganci.

Batun karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2025 a wuce wasanni.

Birnin Rabat, babban waje ne mai tasiri a harkokin diflomasiyya da kwallon kafa, ya zama abin tasiri da alfahari a duniya. Kasar ta riga ta zama hedkwatar kungiyoyin wasanni na Afirka da dama kuma ta ba da jari mai yawa a horo, ta hanyar Mohammed BI Academy ko kuma hadin gwiwa da wasu kungiyoyin Afirka.

Hadin gwiwar karbar gasar cin kofin duniya da za a yi a 2030 tare da Spain da Portugal babu shakka ya nuna yadda kasar ke da tasiri a gudanar da manyan wasannin kwallon kafa a duniya.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax November 6, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025 Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gasar cin kofin kofin duniya da gasar cin kofin zagaye na biyu rashin nasara a wasannin da kwallon kafa Ibory Coast gasar kofin

এছাড়াও পড়ুন:

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang, wakilin cinikayyar kasa da kasa na ma’aikatar kasuwanci kuma mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya gana da tawagar cinikayyar kayan noma ta Amurka a birnin Beijing a jiya Talata 4 ga watan Nuwamb, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da cinikayyar kayayyakin noma, da sauran batutuwa masu alaka.

Li Chenggang ya bayyana cewa kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka tana da alfanu ga kasashen biyu da kuma duniya baki daya. Tun daga watan Mayu na wannan shekarar, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu sun tattauna har sau biyar bisa jagorancin muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda hakan ya karfafa daidaituwar alakar tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka. Wannan ya tabbatar da cewa, Sin da Amurka suna da yakini a kan ci gaba da samun daidaito, girmamawa, da kuma cin gajiyar juna, kuma za su iya samun mafita a kan matsaloli ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.

A nasu bangaren, membobin tawagar ta Amurka sun bayyana cewa kasar Sin muhimmiyar kasuwa ce ta fitar da kayan noma na Amurka, kuma manoman Amurka suna girmama hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kasar Sin, kana suna da niyyar hada hannu don fadada hadin gwiwa da kasar Sin. Sun kara da cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya mai dorewa tsakanin kasar Sin da Amurka tana da matukar muhimmanci ga cinikin kayan noma tsakanin kasashen biyu, kuma suna fatan ci gaba da samun kyakkyawan yanayin bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin November 5, 2025 Daga Birnin Sin Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya November 5, 2025 Daga Birnin Sin An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou November 5, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya
  • Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna
  • Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
  • Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League
  • Ajax ta kori kocinta John Heitinga
  • Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax
  • Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
  • Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja