An gabatar da kundin dokar hana cin zarafin mata a Gombe
Published: 27th, July 2025 GMT
A ƙoƙarinta na daƙile cin zarafin mata da yara, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus, ta gabatar da kundin dokar hana cin zarafi mata (GBV) ga Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar III, domin samun goyon bayan sarakunan gargajiya wajen aiwatar da dokar a matakin ƙasa.
Taron da aka gudanar a zauren Ƙaramar Hukumar Gombe ya samu halartar manyan jami’ai, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma.
LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSFA wajen taron, Kwamishinar ta jaddada cewa dokar na buƙatar goyon bayan al’umma gaba ɗaya, musamman sarakunan gargajiya, waɗanda ke da tasiri wajen sauya tunanin jama’a da inganta tarbiyya.
Da yake karɓar daftarin dokar a madadin Sarkin Gombe, Ɗan Lawan Gombe, Dokta Sani Adamu Jauro, ya bayyana cikakken goyon bayan Masarautar Gombe kan wannan dokar.
Ya ce, “Mai Martaba na tare da wannan yunƙuri, kuma masarauta za ta haɗa kai da gwamnati da ƙungiyoyi wajen kare haƙƙin mata da yara.”
A nata jawabin, Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus ta bayyana cewa, “Sarakunan gargajiya suna da matuƙar muhimmanci a wannan yaƙi, domin suna da ikon canza dabi’u da kuma tabbatar da bin doka a cikin al’umma.”
Shugaban Kwamitin Majalisar Dokokin Gombe kan Harkokin Mata, Mista Gabriel Galadima, ya tabbatar da cewa an fara aiwatar da dokar bayan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya rattaba hannu a kanta.
Ya ce, “Wannan doka ta shafi kowa da kowa wadda ba sani ba sabo ce kuma babu wanda zai tsallaka ta.”
Shi ma, Shugaban Karamar Hukumar Gombe, Barrista Sani Ahmad Haruna, ya nuna goyon bayansa kan dokar tare da alƙawarin wayar da kai, tallafa wa waɗanda abin ya shafa, da kuma inganta sauyin dabi’u a cikin al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Cin Zarafin Mata jihar Gombe goyon bayan
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Eu Sun Fara Tattaunawa A Istambul
Jami’an diblomasiyya na kasashen Iran da kuma na tarayyar Turai 3 wato Faransa da Jamus da kuma burtaniya sun fara tattaunawa gaba da gaba bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka kai mata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta kara da cewa wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci don zasu tattauna kan shirin makamashin nukliyar kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arzikin da su dora mata saboda shirinta na makamshin nukliya. Har’ila yau ana ganin tattaunawar ta Istambul shi zai fayyace makomar dangantaka tsakanin Iran da tarayyar Turai gaba daya nan gaba.
Labarin ya kara da cewa tarunn yana gudana ne a cikin ofishin jakadancin kasar Iran dake birnin Istambul kuma Majid Takht-ravanci da kuma Kazem Ghariba abadi , mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran ne zasu jagoranci tawagar Iran a tattaunawar.
Kuma tattaunawar zasu maida hankali ne kan al-amura guda biyu. Shirin nukliyar kasar Iran da kuma dauke mata takunkuman tattalin arziki wadanda turawan suka dora mata.
Kafin taron dai ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, matsayin Iran bai sawya ba, dole ne tashe makamashin Nukliya a cikin gida ya zama cikin shirin makamashin nukliya na kasar Iran. Ya kuma ce duk wani kokari na amfani da SnapBack zai fuskanci maida martani mai tsanani ga wadannan kasashe.