Osimhen, wanda ya koma Galatasaray daga Napoli, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarorin ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya, ciki har da lashe kofin ƙalubale.

A yanzu haka, shi ne ɗan wasan da ya fi ci wa Galatasaray ƙwallaye a dukkanin da ta ke bugawa a bana, ya bar sauran fitattun ’yan wasa irin su Leroy Sane da Mauro Icardi a baya.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025 Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a Tanzaniya

An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya.

A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba.

An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump

Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.”

Baƙin da aka gayyata ne kawai aka bai wa damar halartar rantsar da Shugaba Hassan a bikin da aka haska duk da katse intanet, yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar kan sakamakon zaɓen.

An ayyana Hassan, wadda ta hau mulki a shekarar 2021 bayan rasuwar tsohon shugabanta, a matsayin wadda ta lashe zaɓen Larabar makon da ya gabata da kashi 97.66% na ƙuri’un da aka kaɗa.

Sai dai ’yan hamayya sun yi watsi da sakamakon kan zargin maguɗi, suna mai cewar an yi amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima kan masu bore bayan ɓarkewar zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓen.

Hassan, mai shekaru 65, ta tsaya takara ne kawai da ’yan takara daga ƙananan jam’iyyu bayan da aka hana manyan masu ƙalubalantarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu shiga takarar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja
  • DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa
  • Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka
  • Fitaccen ɗan wasan tseren mota Jenson Button zai yi ritaya
  • Fitaccen ɗan wasan tseren motoci Jenson Button zai yi ritaya
  • Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani
  • Sinner da Alcaraz za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu
  • Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar Nijeriya
  • An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a Tanzaniya