Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna
Published: 19th, September 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.
Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi.
Shugaba Tinubu ya gana da uwargidan marigayin, Aisha Buhari, da sauran ‘ya’yansa, inda ya sake yi musu ta’aziyya.
Ya kuma tabbatar wa Aisha Buhari cewa zai ci gaba da kula da ayyukan alheri Buhari ya bari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Aisha Buhari Buhari Iyalai Ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027
A ranar Litinin jami’an tsaro da dama sun hallara a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja yayin da Abdulrahman Mohammed Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa ta Tsakiya), ya yi ikirarin cewa, ya karɓi mukamin Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na Kasa a yayin da rikicin shugabancin Jam’iyyar ke kara tsananta. Kwamitin gudanarwar jam’iyyar na ƙasa (NWC) da ke ƙarƙashin jagorancin Samuel Anyanwu ne ya naɗa Mohammed a matsayin muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na ƙasa bayan sauke Umar Damagum, da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, a matsayin wani mataki na adawa da NWC da Damagum ke jagoranta suka yi a baya. Kafin isa sakatariyar PDP da ke Wadata Plaza, Mohammed da magoya bayansa sun taru a ofishin jam’iyyar na Babban Birnin Tarayya (FCT), inda ya tabbatar da sabon matsayinsa kuma ya yi wa ‘ya’yan jam’iyyar jawabi. “A yau, mun dauki nauyin dawo da tsari da hadin kai a cikin babbar jam’iyyarmu,” in ji shi. “PDP ta ‘ya’yanta ce, kuma babu wani mutum ɗaya tilo da zai riƙa juya ta yadda yake so.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso November 3, 2025
Labarai NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan November 3, 2025
Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025