Majalisa ta ɗage ranar dawowarta zuwa 7 ga watan Oktoba
Published: 23rd, September 2025 GMT
Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025.
Karin bayani na tafe..
.উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dawowa daga hutu
এছাড়াও পড়ুন:
Likitoci sun wayar da kan mata kan cutar Sankara a Gombe
Ƙungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) tare da Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Gabas (NEDC), sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kan mata game da cutar sankara a Jihar Gombe, domin kare mata daga kamuwa da cutar.
Dokta Halima Usman Faruk, ɗaya daga cikin likitoci mata da suka halarci wajen taron ta ce, cututtukan sankarar nono da bakin mahaifa na kashe mata da dama a duniya, musamman a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya.
Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri“A Gombe kawai, ana samun aƙalla sabbin mata bakwai masu fama da sankara a duk mako.
“Don haka yana da muhimmanci mata su rika zuwa asibiti idan suka ga wani canji a jikinsu,” in ji ta.
Ita ma Dokta Hauwa Adamu Saurayi, ta ce za su gudanar da gwajin sankara kyauta ga mata 500, musamman masu shekaru tsakanin 15 zuwa 49.
“Sankara ba ta da magani nan take, amma idan aka gano ta da wuri, ana iya samun waraka cikin sauƙi,” ta bayyana.
Matan da suka halarci taron sun yaba da wannan shiri, inda suka bayyana cewa ya ƙara musu ilimi kan yadda za su kare kansu.
Wannan yaƙi da cutar sankara da MWAN da NEDC suka shirya na taimakawa wajen inganta lafiyar mata a Jihar Gombe.