Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro
Published: 6th, November 2025 GMT
Akpabio ya mayar da martani cewa ba su da niyyar ɓata lokaci, inda ya ce, “Ba zan jira kowa ba, saboda da zarar an tantance su, ba za a sake ganinsu ba.”
Daga nan sai ‘yan majalisar suka shiga zaman sirri domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da Trump ya yi iƙirarin ana kisan Kiristoci a Nijeriya — Ndume
Sanata Ali Ndume ya ce jahiltar halin da Najeriya ke ciki ne ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ana kisan Kiristoci a ƙasar.
Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise ranar Talata.
Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsuSanatan ya ce maganganun Trump sun nuna rashin cikakken fahimtar yadda matsalar tsaro take da sarƙaƙiya a Najeriya.
Ya ce matsalar rashin tsaro a ƙasar ta shafi al’umma baki ɗaya ba tare da la’akari bambancin addini ba, yana mai cewa “mutane daban-daban ne ke fuskantar hare-hare daga ‘yan ta’adda, ba Kiristoci kaɗai ba.”
Sanatan ya ƙara da cewa kamata ya yi shugabannin ƙasashen waje su riƙa neman cikakken bayani kafin su yi maganganu da ka iya tada hankali, musamman kan lamurran da suka shafi addini da tsaro.
“Trump bai fahimci haƙiƙanin abin da ke faruwa a Najeriya ba. Matsalar nan ta wuce batun addini, domin dukkan al’ummomi na cikin halin tsoro da fargaba saboda ayyukan ‘yan ta’adda,” in ji Ndume.