Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League
Published: 6th, November 2025 GMT
Ɗan wasan gaba na Nijeriya, Victor Osimhen, ya sha gaban fitattun ‘yan wasa irin su Erling Haaland, Harry Kane, da Kylian Mbappé a yawan zura ƙwallaye a gasar Champions League ta bana.
Osimhen ya cimma wannan nasarar ce bayan ya zura ƙwallaye uku rigis a ragar Ajax a wasan zagaye na huɗu na gasar.
Ajax ta kori kocinta John Heitinga Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a YobeWannan ya kai adadin ƙwallayensa zuwa shida, yayin da Haaland, Kane da Mbappé ke da ƙwallaye biyar-biyar kowannensu.
A watan da ya gabata, Osimhen ya kuma zura ƙwallaye uku a ragar Jamhuriyyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026, abin da ya ƙara masa farin jini a duniya.
Ɗan wasan da yanzu haka yake bugawa Galatasaray na Turkiyya, yana jan hankalin manyan kungiyoyi da dama a Turai, ciki har da Barcelona, wadda ke neman ƙwararren mai zura ƙwallaye domin cike gibin da ke cikin tawagarta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Harry Kane zura ƙwallaye
এছাড়াও পড়ুন:
Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka
Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta Super Eagles, Eric Chelle, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Nigeria za ta lashe kofin nahiyar Afrika na 2026.
Gasar da za a buga a kasar Maroko, Challe ya jadda kwarin gwiwarsa, bisa kafa hujja da zaratan yan wasan da Nigeria ta ke da su.
Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, karo na 35 daga ranar 21 ga watan Disamba da tawagogi 24 za su fafata, domin lashe babban kofin tamaulan na Afirka.
Wannan shi ne karon farko tun 1988 da Maroko ta karɓi baƙuncin wasannin babbar gasar tamaula ta Afirka da take fatan gudanar da bikin da zai ƙayatar da duniya.