Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko
Published: 8th, November 2025 GMT
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano:
Haduwa da kawayen banza da kuma kuntatawa da wasu malaman suke nuna musu, saboda kin amincewa da su na bukatun da suke nema a wajensu. Da yawa iyayen ba sa tsayawa su saurari matsalolin ‘ya’yansu kan abin da ke damunsu a makaranta, da kuma rashin bibiyar karatunsu da abokansu.
Sunana Aisha Isah Gama (Mai Waka), Jihar Kano:
A gaskiya abin da ke janyo wa baya wuce gurba tattun abokai, har da lefin malamai saboda malami ne za ka ga ya kulla soyayya da daliba, kin ga matsala ta farko kenan, sai mu’amala da kawaye marasa tarbiyya, za ki ga baki ragi ‘yar ki da komai ba, amma kawaye sun bata ta. Shawara iyaye mu kula da ‘ya’yanmu, mu ja su a jiki su zama abokan mu, mu rika tunawa kiwo Allah ya ba mu kuma zai tsayar damu ya yi mana tambaya akan kiwon da ya bamu, mu raba su da kawaye.
Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Suleja, Jihar Neja:
Sautari malamai su ne silar lalacewar dalibai akowane makaranta, daga na islamiyar har na bokon. Ka ga malami ya rasa wacce zai yi soyayya da ita sai dalibar sa, duk da ba haramun bane, amma ba sa bin hanyar da ya dace wajan neman soyayyar daliban nasu. Malamai su ne silar lalacewar wasu daga cikin dalibai, daga lokacin da malami ya nuna kwadayi akan abin hannun dalibar sa walau surar da Allah yayi mata ko kuma abun hannuta (kudi) babu magnar tarbiyya a nan wajan. Sautari babu kyau, saboda duk inda aka ce malami to fa matsayin uba yake ga dalibansa. Su ma kuma dalibai su kasance masu kamu kai da nuna kyakkyawan tarbiyya a duk inda suke.
Sunana Hafsat Sa’eed:
Sai dai in ba tarbiyya suka samu tun farko ba,idan har sun samu tarbiyya, kuma an magance musu matsalolin da ba za su ga wani abu su yi sha’awa ba, ba na tunanin yaro zai lalace. Amma rashin hakan yaro na iya shiga cikin wani yanayi. Wasu kuma akwai tarbiyyar amma sakamakon haduwa da kawaye sai su canja, domin kawa tana iya canja kawa a lokaci daya. Amma akwai wadanda jarrabawa ce, idan Allah ya jarabce ka babu yadda za ka yi sai ka karba ka yi ta addu’a.
Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:
Na farko dai akwai matsalar Tarbiyya wadda ita ce tushen komai, sannan kuma da rashin gata ga wasu, wasu kuma neman abin duniya ne yake kai su ga lalacewa. Munanan abokai kan iya bata abokansu, haka kuma rashin bibiyar iyaye akan lamarin ‘ya’yansu har sai sun fada wani hali. Iyaye su sa hankali da lura akan yaransu, kuma su dage da yi musu addu’a, kuma su san su waye abokan ‘ya’yansu.
Sunana Fatima Nura kila, Jihar Jigawa:
Abin da yake janyo wa mafiya yawa shi ne, san zuciya, kusan shi ne kaso 70% na lalacewar dalibai mata a makarantu. Yana faruwa ne mata sun dau karya sun dorawa rayuwarsu, wata iyayenta rufin asiri gare su, za ta ce sai ta yi abin da kawarta ta yi, bayan samun iyayen kowanne daban. Shawarar ita ce, a kodayaushe mu mata mu daina kallan saman mu, a kodayaushe mu rika kallon kasan mu, hakan shi ne zai sa mana wadatar zuci.
Sunana Hassana Sulaiman, Hadejia, A Jihar Jigawa:
Daga cikin abin da ke kawo lalacewar dalibai musamman ma mata a makarantun boko da kuma islamiyya cikin al’umma, wani lokacin rashin sanin su kansu ne da iyayen basu fiya duba da lamuran yaran nasu matan ba. Dalilin lalacewar wasu daga cikin dalibai a wannan lokacin bai huce na kawaye ba. Saboda kawaye suna taka muhimmiyar rawa wani lokacin fiye ma da iyayensu. Ya kamata iyaye musamman mata, su zama kawaye ga ‘ya’yan nasu dan ta haka ne ‘ya’yan nasu matan za su iya sakin jiki da su suna zaman fira tare a hakan iyayen za su fahimci su waye ne ma yaransu, kuma wani abu ne a ransu wanda za su iya basu shawarar yadda za a magance matsalar maimakon lalacewar su ta sanadiyyar kawaye.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi, Jihar Kano:
Yawanci soyayya da malamai ke yi da dalibai shi yake jawo wa. Kin ga kawaye sune kan gaba wajen canja wa yara dalibai tarbiyya da kuma ita soyayyar da malaman ke shinfidawa da yaran. Iyaye dai su rika kulawa da tarbiyyar ‘ya’yansu dan kuwa amana ce Allah ya dora a hannunsu.
Sunana Nabila Dikko, Argungu, Jihar Kebbi:
Lalacewar ɗalibai mata na yawaita ne saboda rashin kulawar iyaye, rinjayar abokai marasa tarbiyya da amfani da kafafen sada zumunta ba tare da iyaka ba. Wasu suna da kamun kai saboda tarbiyyar gida, wasu kuma babu. Shawara, iyaye su kula da ‘ya’yansu, dalibai kuma su tsare mutuncinsu, su mayar da hankali ga karatu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu
Majalisar Dattawa ta dakatar da aikin tantance Dokta Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa domin zama minista, sakamakon rashin gabatar mata da rahoton jami’an tsaro a kansa.
Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce ba za su ci gaba da tantancewar ba sai an samu cikakken rahoto daga hukumomin tsaro.
Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a KanoA ranar Talata ce Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar sunan Mista Udeh, ɗan asalin Jihar Enugu cikin wata wasiƙar neman sahalewarta.
“Ina farin cikin miƙa sunan Dokta Kingsley Tochukwu Ude, SAN, domin tabbatar da shi a matsayin minista. Ina fatan majalisar za ta yi la’akari da wannan buƙata cikin gaggawa kamar yadda aka saba,” in ji wasiƙar shugaban ƙasan.
Tinubu ya naɗa Udeh ne bayan murabus ɗin da tsohon Ministan Kimiyya, Uche Nnaji ya yi, bayan zargin da aka yi masa na gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta bogi, wanda kuma shi ne minista ɗaya kacal daga Jihar ta Enugu
Mista Udeh wanda yanzu haka shi ne Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Enugu, ya shahara da ƙwarewa a fannin doka da kare haƙƙin ɗan Adam.