Aminiya:
2025-11-05@07:55:23 GMT

An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump

Published: 5th, November 2025 GMT

An yi musayar yawu a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin Shugaban Amurka, Donald Trump, na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Zaman majalisar ya biyo bayan sanarwar Trump da ke bayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa Mai Ƙalubale Na Musamman,” yana zargin Gwamnatin Tarayya da bari a ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar.

DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU

Batun ya taso ne a ƙarshen zaman majalisar na ranar Talata, lokacin da Akpabio ya shaida wa ’yan majalisar cewa ’yan Najeriya na son jin matsayar Majalisar Dattawa kan lamarin.

Sai dai ya ce ba za a ɗauki matsaya ba har sai Gwamnatin Tarayya ta gabatar da matsayinta a hukumance kan batun.

“Ni waye da zan mayar wa Trump da martani?” in ji Akpabio cikin tambaya, yana mai bayyana cewa Majalisar Dattawa ba za ta tattauna batutuwa ba sai an gabatar da su ta hanyar da ta dace.

Ya ƙara da cewa duk da cewa ’yan Najeriya na son majalisar ta mayar da martani, za su jira bayanai a hukumance kafin su ɗauki mataki.

Sai dai kalamansa sun jawo martani kai tsaye daga mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin.

“Kar ka ji tsoro, ni zan yi magana. Ba na tsoron Trump. Zan faɗi ra’ayina,” in ji Barau.

Ya ci gaba da cewa, “Ni ɗan Najeriya ne, ɗan majalisa, kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa mai cikakken ’yanci. Ba na tsoron Trump. Kada ku ji tsoron Trump. Kuna da ’yancin faɗar ra’ayinku a kansa. Mu ƙasa ce mai cikakken ’yanci. Yana yaɗa ƙarya game da ƙasarmu, kuma muna da ’yancin musanta hakan.

“Idan ka ce ba za ka yi magana ba, hakan daidai ne, amma abin da nake ƙoƙarin faɗa shi ne kada ka ji tsoronsa.”

Akpabio ya katseshi yana mai cewa, “Na ce ba na tsoro. Yaya za a ce Shugaban Majalisar Dattawa na ƙasa zai ji tsoron Trump?”

Ya ƙara da cewa, “Ka fahimta, ka faɗi ra’ayinka, amma kada ka bari mutane su danganta maka abin da ba ka faɗa ba. Amma idan kana so na faɗa yanzu, zan faɗa. Amma ka saurara, zan faɗi abin da muka tattauna ne kawai.”

Daga nan sai Akpabio ya juya ga Akawun Majalisar, yana umarnin a goge kalaman Barau daga kundin rubuce-rubucen majalisar, yana mai cewa Barau ya “fita daga layin magana.”

Sai dai Barau bai nuna damuwa ba, ya tashi ya nufi kujerar Akpabio, inda suka yi gajeriyar tattaunawa a sirrance da ta ja hankalin sauran ’yan majalisar, kafin ya koma kujerarsa.

Aminiya ta rawaito cewa kalaman Trump, da Sakataren Yaƙi na Amurka, Pete Hegseth, a shafin a X cewa kasar na “shirin ɗaukar matakin soja,” sun haifar da fushi a fagen siyasa da diflomasiyya.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya musanta zargin Trump, yana mai jaddada cewa Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya da ke ba da ’yancin addini da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Haka kuma, ƙasar China ta nuna rashin amincewa da kalaman Trump, tare da bayyana goyon bayanta ga Najeriya, tana mai bayyana ta a matsayin “abokiyar”.

Beijing ta gargaɗi cewa babu wata ƙasa da ya kamata ta yi amfani da batun addini ko ’yancin ɗan adam a matsayin uzuri don tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata ƙasa mai ’yanci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Barau Shugaban Majalisar Majalisar Dattawa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya.

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka

Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa.

“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” in ji Gumi.

Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka.

“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.

Gumi, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.

“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” in ji Gumi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150
  • Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio
  • Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar
  • ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu
  • China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya
  • Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu
  • Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 
  • Trump ya jaddada shirin Amurka na kai hari a Najeriya
  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi