Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi
Published: 5th, November 2025 GMT
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “matukar damuwarsa” kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi akai-akai a zirin Gaza.
Da yake bayyana ga manema labarai a gefen taron koli na biyu na duniya kan ci gaban zamantakewa a Doha jiya Talata, Guterres ya ce: “Dole ne su dakatar da wadannan ayyuka, kuma dukkan bangarorin dole ne su mutunta sharuddan dake kunshe a matakin farko na yarjejeniyar zaman lafiya.
“Muna aiki tukuru don kara taimakawa mutanen yankin Gaza; muna goyon bayan mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dawo da alaka tsakanin Gaza da Yammacin Kogin Jordan,” in ji Mista Guterres.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, hare-haren Isra’ila a Gaza na ci gaba da kashe Falasdinawa da dama kowace rana.
A makon da ya gabata, hare-haren Isra’ila a fadin Gaza sun kashe mutane sama da 100, ciki har da yara 46.
Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila na tsawon shekaru da dama kuma ya jaddada ‘yancin al’ummar Falasdinawa na neman ‘yancin kai.
Ya jaddada cewa, “Kada mu manta da bukatar kafa wata hanyar siyasa mai inganci don kawo karshen mamayar.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Karon farko an zabi Musulmi magajin New York, birni mafi girma a Amurka November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba
Kungiyoyin agaji da dama na kasashen duniya sun yi gargadin cewa tallafin da ake bai wa yankin Gaza bai isa ba kusan wata guda bayan da aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da yankin ke ci gaba da fuskantar matsalar abinci da matsugunai yayin da hunturu ke gabatowa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta nuna cewa rabin kayan abinci da ake bukata ne kawai ke isa yankin da aka killace.
Abeer Etefa, babban mai magana da yawun WFP, ya bayyana cewa hukumar ta isar da tan 20,000 na abinci, kusan rabin adadin da ake bukata, kuma ta bude wuraren rarraba abinci 44 daga cikin 145 da aka tsara.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Jinkai (OCHA) a Falasdinu shi ma ya ba da rahoton cewa karancin mai, musamman iskar gas, yana kara ta’azzara rikicin, wanda ya tilasta wa sama da kashi 60% na mutanen Gaza su dafa abinci ta hanyar kona shara, wanda hakan ke haifar da babbar barazana ga lafiyar jama’a.
A ranar 10 ga Oktoba, tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani ya fara aiki a Zirin Gaza.
An yi wannan yarjejeniyar tsagaita wuta ne domin a samu kwararar kayan agaji zuwa yankin da ke da cunkoson jama’a, inda aka tabbatar da yunwa a watan Agusta, kuma kusan dukkan mazauna yankin miliyan 2.3 sun rasa gidajensu sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra’ila ta kai musu.
A cewar kiyasin Majalisar Dinkin Duniya, kashi 81% na kayayyakin more rayuwa na Gaza sun lalace ko kuma sun ruguje.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila November 5, 2025 Shugaban Najeriya Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU November 5, 2025 Kakakin Dakarun IRGC Ya Ce; Ko Kadan Amurka Ba Abar Amincewa Ba Ce November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci