Aminiya:
2025-11-07@20:56:13 GMT

Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu

Published: 7th, November 2025 GMT

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai wajen magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiyar ƙasa.

Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai

A wata sanarwa da Tinubu ya fitar a shafinsa na sada zumunta, a ranar Juma’a, ya ce ƙalubalen tsaro a Najeriya, da suka haɗa da ta’addanci da aikata laifuka, ana magance su da sabbin tsari da sauye-sauyen dabarun dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

“Haƙiƙa muna fuskantar ta’addanci – ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta kusan shekaru ashirin, kuma ba za mu ja da baya ba, za mu yi nasara a kan ta’addanci kuma mu yi iƙirarin samun nasara a wannan yaƙin, ba za mu taɓa yin sulhu harkar tsaro ba.

“Najeriya ƙasa ɗaya ce mai haɗin kai, mun tashi tare, mun ci gaba tare, kuma mun ƙi yanke ƙauna domin tabbatar da ƙuduri.

“Aikin da ke gabanmu yana da yawa, amma duk da haka ƙudurinmu ya fi girma, za mu ci gaba da ɗorewa tare da inganta nasarorin da muka samu na sake fasalin ƙasa da kuma samar da ci gaba a Najeriya.

“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba kuma ba za mu bar wani abu ba a cikin aikinmu na kawar da masu aikata laifuka a cikin al’ummarmu, muna kira ga abokan haɗin gwiwarmu da su tsaya tsayin daka tare da mu yayin da muke ƙara faɗaɗa yaƙin da muke yi da ta’addanci, mun samu gagarumin ci gaba a cikin shekaru biyu da suka gabata, kuma za mu kawar da wannan barazana.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu matsalar tsaro Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

Akpabio ya mayar da martani cewa ba su da niyyar ɓata lokaci, inda ya ce, “Ba zan jira kowa ba, saboda da zarar an tantance su, ba za a sake ganinsu ba.”

Daga nan sai ‘yan majalisar suka shiga zaman sirri domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matsalar Tsaro: Mun sami gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu
  • Sojin Amurka sun gabatar da shirin ƙaddamar da hari a Najeriya
  • Najeriya ta yi watsi da sanya sunanta cikin jerin kasashen da ake tauye ’yancin addini
  • Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro
  • Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri
  • Gwamnan Kano Ya Yaba Da Matakin Da Sojoji Suka Dauka kan Matsalar Tsaron Tsanyawa