Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho
Published: 6th, November 2025 GMT
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bukaci Amurka da Turai su nuna gaskiya idan suna son sake gina aminci da Iran.
A wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da takwaransa na Iran Mas’ud Pezeshkian, shugaban na Iran ya ce dole ne turai su mutunta ‘yancin Iran kuma su daina gabtar da bukatu da Iran ba za ta taba amincewa da su ba.
Iran ta yi maraba da tattaunawa amma Pezeshkian ya sake nanata cewa, a yanzu ba Iran ce za ta tabbatar da gaskyarta ba, domin ta riga ta yi haka, ya rage kan kasashen turai ne su tabbatar wa duniya cewa da gaske suke yi a cikin abin da suke furtawa.
Duk da haka, ya ce, Iran na ci gaba da fuskantar zarge-zarge marasa tushe da kuma ƙarin takunkumi a ƙarƙashin hujjar cewa tana hankoron kera mkaman nukiliya.
Pezeshkian ya jaddada cewa za a iya magance matsaloli ne kawai ta hanyar tattaunawa da mutunta juna, ba ta hanyar tilastawa ko barazana ba.
“Inda za a iya magance rashin fahimta ta hanyar yin amfani da hankali, me ya kawo maganar yin amfani a karfi da kashe-kashe da rusa gine-gine da ababen mor rayuwa na al’ummar kasa.
A nasa bangaren, Macron ya gode wa Pezeshkian saboda matakan da aka dauka don aiwatar da yarjejeniyoyin da suka gabata kuma ya bayyana niyyarsa ta yin aiki don samar da sabon tsari na tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Yammacin duniya.
Ya ce ci gaba da tattaunawa yana da mahimmanci don gina gaskiya da aminci, da dage takunkumi, da kuma inganta dangantakar kasashen biyu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar November 6, 2025 Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce wasu shugabannin kasashen waje za su hallara a birnin Shanghai, domin halartar baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na takwas, wanda zai gudana tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga watan nan na Nuwamba.
Kakakin wadda ta bayyana hakan a Litinin din nan, ta ce cikin shugabannin da ake sa ran za su halarci bikin bude baje kolin na CIIE, da sauran ayyuka masu nasaba da shi bisa gayyatar da aka yi musu, akwai firaministan kasar Georgia Irakli Kobakhidze, da na Serbia Djuro Macut, da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Abbas Tajudeen, da shugaban majalisar gudanarwar kasar Slovenia Marko Lotric. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA