Za a ɗauki nauyin ɗalibin BUK don shiga kundin ‘Guinness World Record’
Published: 25th, September 2025 GMT
A wajen ɗalibin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, zane ba kawai sha’awa ba ce kaɗai, face hanya ta shiga kundin tarihin duniya.
A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, Collins zai shiga sahun tarihin duniya yayin da zai yi ƙoƙarin kafa tarihi har guda biyu na shiga kundin ‘Guinness World Record’ a fannin zanen fuska.
Kamfanin Indomie ne zai tallafa wa ɗalibin domin gwada bajintarsa wajen shiga kundin Guinness World Record.
Burinsa shi ne zana fuskar mutane 12 ko sama da haka a cikin minti uku da kuma fuskar mutane 220 ko sama da hakan cikin sa’a guda, inda yake ƙoƙarin ƙwace kambun da Emilia Zakonnova, wadda ke riƙe da shi, wadda ta zana fuskar mutane 12 cikin minti 3 a ranar 30 ga watan Yuli, 2025.
Ya taɓa gwada irin wannan a shekarar 2024 ammabai kai gayin nasara ba, wannan yasa ya ƙara himma da ƙaimi don gwada sa’arsa.
“Na koyi darusa da yawa daga yunƙurina na farko. Yanzu na shirya, na mayar da hankali kuma na ƙuduri aniyar cimma nasara.
“Da goyon bayan da kamfanin Indomie ya ba ni, ina da tabbacin za mu kafa tarihi tare,” in ji Collins.
Matashin ya ɗauki sa’o’i da yawa yana ɗaukar horo a fannin zanen fuska, yana kuma daidaita tafiyar da karatunsa.
Kamfanin da ke samar da taliyar ‘yan yara wato Indomie ce ta ɗauki nauyin tallafa wa ɗalibin domin cikar muradinsa.
Har ila yau, kamfanin ya sha alwashin ci gaba da tallafa wa matasa a fannin ƙirƙira a faɗin Nijeriya.
Taron da aka shirya gudanarwa a Jihar Kano a ranar tunawa da samun ‘Yancin Kan Nijeriya, zai haɗa ɗalibai da iyalai da masoya fasaha, waɗanda za su bayar da fuskokinsu da goyon bayansu domin cikar burin matashin.
Kamar yadda taken yake: “Mafarki mai yawa na haifar da nasarori masu yawa.”
A ranar 1 ga watan Oktoba, idanun duniya za su karkata zuwa Kano domin shaida ganin Collins Whitworth zai kafa tarihi.
Bayan samun lambobin yabo masu yawa, wannan yunƙuri wata babbar nasara ce a fannin ƙirƙira da fasaha a Nijeriya da idon duniya.
Idan ba a manta ba a makom da ya gabata ne, fitacciyar mai girkin nan Hilda Baci, ta kafa sabon tarihi a fannin girki.
Matashiyar ta girka shinkafa dafa-duka har buhu 200 kuma a cikin tukunya mafi girma.
Tuni dai kundin Guinness World Record ya amince da sabon tarihin da ta kafa a fannin girki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibi
এছাড়াও পড়ুন:
Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
Hukumar tsaro ta DSS ta zargi dan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin kasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karbar Naira miliyan 50 daga kudin fansar fasinjojin.
Ana zargin Tukur Mamu da karbar kudin ne daga jagoran ’yan bindigar da ake kira da “Shugaba”.
Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan KebbiMamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana aikin kwamitin babban hafsan tsaron kasa da aka kafa domin tattaunawa da masu garkuwa da mutanen, musayar saƙonnin murya da mai magana da yawun Boko Haram, da sauransu.
A ci gaba da shari’ar a ranar Talata, shaida na hukumae ta DSS na shida ya shaida wa kotu cewa ƙungiyar ta’addan ta nemi Mamu ya koya musu yadda ake buɗe shafin yanar gizo domin gudanar da ayyukansu.
Tun da farko, DSS ta bayyana cewa Mamu ya ba da shawara ga ƙungiyar ’yan ta’addan da su tattauna kai tsaye da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, ba tare da shiga kwamitin babban hafsan tsaron da gwamnatin tarayya ta kafa ba.
Shaidar ya yi wannan bayani ne yayin fassara saƙonnin murya na Mamu a lokacin da ake yi masa tambayoyi a ƙasar Masar kafin a dawo da shi Najeriya.
A halin yanzu, Mamu ya shigar da Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa kiran shi da dan ta’adda.
Ya ce ya shigar da ƙarar ce kan kiran nasa da dan ta’adda da ministan ya yi, alhali ana tsaka da shari’ar tuhumar laifukan ta’addanci kuma har yanzu ba a kai ga yanke hukunci ba.
Alƙali ya dage shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun 2026, domin amincewa da jawaban ƙarshe na ɓangarorin da abin ya shafa bisa tanadin Sashe na 49 na Dokar da kuma Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.