Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock
Published: 8th, November 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a.
Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya gana da Shugaban Ƙasa ba tare da ’yan jarida ba.
Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800Ganawar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya gana da Archbishop Ignatius Kaigama na Katolikan Abuja, a wani yunƙuri na inganta dangantakar addinai da zaman lafiya a Najeriya.
Ko da yake ba a bayyana abin da suka tattauna ba, amma ganawar ba za ta rasa nasaba da ƙarfafa fahimtar juna tsakanin addinai da kuma bunƙasa haɗin kan ƙasa da ci gaba.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya bisa zargin cin zarafin Kiristoci.
Bayan ganawar, Sarkin Musulmi, ya raka Shugaba Tinubu zuwa sallar Juma’a a Masallacin Fadar Shugaban Ƙasa.
A lokacin huɗubar sallar Juma’ar, limamin masallacin, Alhaji Abdulwaheed Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa zaman lafiya da tsaro.
Ya tunatar da jama’a cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ganawa Sarkin Musulmi Zaman lafiya Shugaban Ƙasa Sarkin Musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro
Akpabio ya mayar da martani cewa ba su da niyyar ɓata lokaci, inda ya ce, “Ba zan jira kowa ba, saboda da zarar an tantance su, ba za a sake ganinsu ba.”
Daga nan sai ‘yan majalisar suka shiga zaman sirri domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA