Leadership News Hausa:
2025-11-05@23:35:12 GMT

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Published: 6th, November 2025 GMT

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

 

A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan take ni ma na zaro wayata, muka ci gaba da kashe hotuna ni da abokin aikina.

Na yi kokarin nuna kawaici a kan yadda yanayin ya shaukantar da ni, amma sai na ga abokin nawa ya fi ni “jazabancewa”, domin shi ya fi ni yawan yin “style” na daukar hoton da kuma yawan hotunan da muka dauka.

 

Wani abu da na lura da shi a kasar Sin shi ne, ba kawai a manyan birane ba, hatta a garuruwa na gundumomi, kasar ta samar da lambuna masu furanni da koramu da itatuwa masu ban sha’awa, inda iyalai suke zuwa domin shakatawa musamman da maraice bayan tasowa daga makaranta.

 

Ni dai, idan wani mai yawon shaktawa ya tambaye ni, wane lokaci ne mafi dacewa ya kawo ziyara kasar Sin, zan ce masa ka zo a lokacin “yanayi mai launin zinare”, watau a lokacin kaka, musamman daga karshen watan Oktoba kafin shiga yanayin hunturu sosai lokacin da wannan launi zai sauya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya November 5, 2025 Daga Birnin Sin An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou November 5, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE  November 5, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi

Shugaban kasar Mali Assimi Goita ya yi wa al’ummar kasar jawabi akan karancin man fetur da ake fama da shi a kasar da kuma yadda masu ikirarin Jihari suke killace motocin dakon makamashi.

An fara samun kamfar man fetur ne a kasar Mali wacce ba ta da iyaka ruwa, da masu ikirarin jihadi su ka tare kan iyaka da hana tankokin man fetur shiga cikin kasar.

Goita ta bayyana cewa:

“ A duk lokacin da za a dauko motocin dakon mai, mutane suna mutuwa, ana yin kwanton bauna akan hanya,ana kona motocin da mutane a cikinsu har su kone kurmus.”

Goita ya bayyana haka ne a lokacin dake halartar bikin bude wurin hako ma’adanin “Lithium” a yankin Bougouni a kudancin kasar.

Kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam Wal-Muslimin mai alaka da alka’ida ce take killace tankokin dakon man fetur da hana su zuwa gidajen mai.

Tun a cikin watan Satumba ne dai kungiyar mai dauke da makamai ta sanar da hana shigar da tankokin man fetur cikin kasar.

Sojojin kasar ta Mali dai suna yi wa tankokin jigilar man fetur rakiya daga kan iyaka har zuwa birnin Bamako, tare da yin amfani da jiragen yaki domin kai wa masu dauke da makaman hari.

Shugaban kasar ta Mali ya kira yi al’ummar kasar da su rage gudanar da tafiye-tafiye domin rage karfin tasirin kamfar man fetur din.

A cikin birnin Bamako ana ganin dogayen layukan ababan hawa a cikin gidajen man fetur.

Tun bayan juyin mulki a kasar, karancin man fetur din yana a matsyain koma baya mafi girma da kasar take fuskanta.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi  November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
  • Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi
  • Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 
  • DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai
  • Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
  • Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
  • Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai
  • Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka
  • NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Kasar Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?