Dole Faransa ta ɗauki haddasa mana rikici Tun daga shekarar 1899 Faransa take — Nijar
Published: 28th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi zargin cewa tun daga shekarar 1899 Faransa take fafutikar tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel.
Firimanistan Jamhuriyyar Nijar, Ali Lamine Zeine, ya yi wannan caccakar ce kan Faransa a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na Amuka.
Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da ɗukar alhakin laifukan da suka aikata” a Nijar tun daga shekarar 1899.
“Tun lokacin da muka fatattaki sojojinsu daga [Nijar] a 2023, gwamnatin Faransa take kitsa wani shiri na ƙarƙashin ƙasa domin wargaza ƙasata,” in ji Ali Lamine Zeine.
Kazalika ya zargi Faransa da “bayar da horo da kuɗi da kuma makamai ga ’yan ta’adda” tare da yunƙurin haifar da “rikicin ƙabilanci” a Jamhuriyar Nijar da yankin Sahel.
Firaministan na Nijar ya ƙara da cewa mahukunta a Paris sun ƙaddamar da wata gwagwarmaya ta watsa “labaran ƙarya da haddasa husuma” da zummar ɓata ƙasarsa da shugabanninta da hukumominta a idanun duniya.
Lamine Zeine ya shaida wa taron UNGA cewa Faransa tana rura wutar rikicin “siyasa tsakanin ƙasata da kuma wasu maƙotanmu,” inda ya ƙara da cewa Faransa tana hana Nijar aiwatar da ayyukan ci-gaba tare da hana hukumomin kuɗinta sakat.
“Wannan ya haɗa da ƙiyayyar da Faransa take nuna mana wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba ta hanyar hana masu son zuba jari na ƙasashen duniya irin su ADB da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a ƙasarmu,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faransa Nijar Faransa take
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025
Daga Birnin Sin Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba October 12, 2025
Daga Birnin Sin Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza October 11, 2025