’Yan bindiga da masu ɗaukar musu bayanai ba su da bambanci — Gwamnan Sakkwato
Published: 9th, September 2025 GMT
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Wurno da Rabah a ranar Litinin da ta gabata, domin jajanta wa al’umma bisa hare-haren da ’yan bindiga ke kai musu.
Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen daƙile matsalar ’yan bindiga a faɗin jihar, inda ya buƙaci mazauna ƙauyuka su riƙa tona asirin duk wanda suka sani yana bai wa ’yan bindiga bayanai, domin hukuma ta ɗauki matakin da ya dace.
Gwamnan ya bayyana irin takaicin da yake ji kan masu kai kai wa ’yan ta’adda bayanai saboda ɗan wani abin da bai taka kara ya karya ba, yana mai cewa hakan rashin kishin ƙasa ne.
Ya kuma gargaɗi duk masu wannan mummunar ɗabi’a cewa ba za su tsira ba a sakamakon wannan sabon tsarin da gwamnatin sa ta fito da shi na kawar da ’yan bindiga daga jihar.
“Mun himmatu don ganin mun zaƙulo waɗannan infoma da suka hana jama’armu zaman lafiya ko ta halin ƙaƙa.
“Don haka muke roƙon jama’a da su bayar da haɗin kai don dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Sakkwato,” in ji gwamna Ahmad.
Gwamnan ya kuma buƙaci limaman Juma’a da sauran malamai da su yi wa’azi a kan irin laifin da ke cikin taimaka wa ’yan bindiga, da matsayin addini kan irin waɗannan ayyukan ɓarna.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jihar Sakkwato yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
Ya ce, masu garkuwa da mutanen sun afka gidansa ne a daren Lahadi a lokacin da mazauna gidan ke shirin kwanciya barci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp