Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya
Published: 6th, November 2025 GMT
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin ƙasa da ƙasa da shari’a ya jaddada muhimmancin kara karfafa dangantakar da ke tsakanin Tehran da Riyadh, yana mai cewa ci gaban kyakkyawar alaƙa tsakanin Tehran da Riyadh ba wai kawai yana da amfani ga ɓangarorin biyu ba ne, har ma zai kara karfafa zaman lafiya a yankin da ma a duniya.
Kazem Gharibabadi ya yi wannan furuci ne bayan ziyarar da ya kai Saudiyya da nufin fadada haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin manyan ƙasashen biyu.
Mataimakin ministan harkokin wajen ya jaddada cewa Iran da Saudiyya, waɗanda ke da alaƙa ta tarihi suna da kyakkyawan matsayi don yin hidima ga al’ummarsu da kuma taka domin ci gaban zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya.
Gharibabadi ya yi cikakken bayani game da ganawarsa da Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Saudiyya, Abdulrahman al Rassi.
Ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa a mataki na yankin da kuma na ƙasa da ƙasa.
Jami’an sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan ƙarfafa muhimmiyar rawar da Ƙungiyar Haɗin Kan Musulmi (OIC) ke takawa.
Gharibabadi ya ce ya jaddada bukatar da ke akwai ga OIC ta taka muhimmiyar rawa wajen magance muhimman batutuwa, ciki har da yin Allah wadai da laifukan mamayar da Isra’ila ta yi a Gaza da kuma cin zarafin da take yi a yankin, tare da fadada hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa
Kungiyar ‘yan tawayen M23 tare da hadin gwiwar kungiyar AFC sun kafa kotunan shari’a a cikin yankunan da suke iko da su a gundumar Kivu ta Arewa.
A garin Goma kungiyar ta sanar da kafa kotuna 378 a fadin yankunan da suke karkashin ikonta, lamarin da gwamnatin Kinshasha ta bayyana a matsyin haramtacce.
Wani makusancin kungiyoyin tawayen dake rike da yankunan gabashin DRF, Elie Mutela ya sanar da cewa; Tsarin mulkin kasar ya tabbatar da cewa bai kamata a bar mutane ba tare da tsarin shari’a ba, wannan ne dalilin da ya sa kungiyoyin M23/AFC su ka kafa kotuna domin yi wa mutane shari’a akan matsalolin yau da kullum.
Tun a ranar 14 ga watan Satumba ne dai aka fara farfado da tsarin shari’ar,tare da zabar alkalan da za su tafiyar da kotunan.
Wani mai rajin kare hakkin bil’adama a yankin Gueul Mamulaka ya ce; Labari ne mai dadi,amma kuma a lokaci daya mai cike da makaki.”
Ya kuma kara da cwa; Da akwai cin karo da juna a cikin abinda M23 take son yin a kafa kotuna da kuma yadda Kinshasha ta ce,hakan ba ya kan doka.
Gwamnatin Kinshasha ta yi tir da abinda kungiyar M23 take yi, tare da da cewa kotunan da za ta kafa ba su wani matsayi na shari’a.
Yankunan gabashin kasar DRC mai arzikin ma’adanai ya dade yana fama da rikice-rikice, da a halin yanzu kungiyar ‘yan tawaye ta M23 da abokan kawancenta suka shimfidi ikonsu a ciki.
Gwamnatin kinshasha dai tana zargin kasar Rwanda da cewa ita ce take goyon baya da taimakon kungiyar ta M23 da kuma ba ta makamai da sojoji. Gwamnatin kasar Rwanda ta sha kore wannan zargin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci