Gwamnatin Kaduna Za Ta Horas Da Ɗalibai 32,000 Sana’oin Hannu A Duk Shekara – Maiyaki
Published: 28th, September 2025 GMT
Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki.
Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun ƙwararrun ma’aikata a bangarorin gine-gine, makamashi, fasahar zamani (ICT), kula da baƙi, da harkokin ƙirƙira.
Shima Shugaban Cibiyar, Malam Husaini Haruna Muhammad, ya jaddada muhimmancin da horon ke da shi wajen dacewa da bukatun kasuwanni da wuraren aiki: “Abin da muke mayar da hankali a kai shi ne samar da daliban da suka kammala karatu waɗanda suke da shirye-shiryen fuskantar kasuwa da wuraren aiki. Kashi 80% na horonmu yana kasancewa ne na aikace-aikace, wanda ke ba wa ɗalibai damar samun ƙwarewar rayuwa ta ainihi a fannonin da suka zaɓa. Wadannan ƙwarewar ba wai kawai sun dace da tattalin arzikin Najeriya ba ne, har ma suna da gasa a matakin duniya. Muna ƙarfafa ‘yan ƙasa musamman mata, masu nakasa da matasa masu rauni da su amfana da wannan dama.”
Tare da kayan aiki da ma’aikata masu ƙwarewa da aka tanada, cibiyar na da niyyar yaye ɗalibai 16,000 a zangon horo na farko, tare da nufin cimma burinta na yaye ɗalibai 32,000 a kowace shekara.
Yace Gwamnatin Jihar Kaduna na kira ga al’ummar jihar da ma wajenta da su yi amfani da wannan dama don samun ƙwarewa da za ta basu damar samun aiki, kafa nasu sana’a, da dogaro da kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan Nuwamba a jihar.
Shugaban Hukumar Kula Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar.
Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan.
Ya ƙara da cewa rigakafin watan Nuwamba za a gudanar da shi ne tare da Makon Lafiyar Uwa, Jariri da Yara (MNCH), inda ake ba mata masu juna biyu kulawar lafiya.
Dakta Sambo ya roƙi goyon bayan kafafen yada labarai domin isar da sako da kuma wayar da jama’a.
A nasa jawabin, Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Mohammed Rahama Farah, ya yaba wa jihar Jigawa bisa rage yawaitar cutar ta shan inna da kashi 58 bisa dari a shekarar 2024.
Sai dai ya yi gargadin ccewahar yanzu cutar na barazana a Najeriya , domin an samu lamura 72 a jihohi 14 a shekarar 2025, don haka akwai buƙatar ƙara faɗaɗa rigakafi.
Rahama Farah ya yi kira shugabannin kananan hukumomi da su sa ido sosai kan yadda ake gudanar da aikin domin tabbatar da nasara, tare da bukar kafofin watsa labarai su ƙara wayar da kai ga iyaye.
Ya kuma yi kira da a ɗauki aikin a matsayin na kowa da kowa domin kawo ƙarshen yaduwar cutar shan inna a Jigawa da sauran jihohin ƙasar nan.
Ita ma da yake jawabi a madadin Hukumar Kula da Lafiyar Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Hajiya Firdaus Aminu ta yaba wa jihar bisa kyawawan shirye-shirye game da shirin yaki da cutar.
Za a gudanar da rigakafin shan innan na watan Nuwamba daga 27 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disamba, 2025.
Aikin, tare da makon MNCH, za su gudana ne ta hanyar ƙungiyoyi 2,015 na ma’aikatan wucin-gadi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.