FIFA Ta Rage Maki, Ta Ci Tarar Kuɗi Kan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta Kudu
Published: 30th, September 2025 GMT
Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ya sanar da matakin da ta ɗauka a kan tawagar ƙwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki, sannan ta ci ta tarar kuɗi.
Kwamitin ya bayyana cewa ƙasar ta karya doka ne ta hanyar amfani da ɗan wasa da bai cancanci buga wasan ba, a fafatawar da suka yi da Lesotho, inda Teboho Mokoena ya taka leda a ranar 21 ga Maris, 2025.
FIFA ta ce amfani da ɗanwasan ya saɓa da sashe na 19 da kundin laifuka na hukumar, sannan ya kuma saɓa da sashe na 14 na kundin shirye-shiryen farko-farko na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026.
FIFA ta ce bayan nazarin binciken da aka gudanar, ta ƙwace nasarar da Afirka ta Kudu ta samu, sannan ta ba ƙasar Lesotho nasara a wasan.
Haka kuma hukumar ta ci Afirka ta Kudu tarar CHF 10,000, sannan shi ma ɗanwasan, Teboho Mokoena ya samu takardar gargaɗi.
Waɗanda aka ladabtar saboda laifukan dai suna da kwana 10 domin ɗaukaka ƙara a gaban kwamitin ɗaukaka ƙara na kwamitin ladabtarwa na Hukumar FIFA.
BBC
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%
An samu wannan raguwar ne sakamakon sauye-sauyen da aka samu a shekarar da muke ciki.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA