Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe
Published: 6th, November 2025 GMT
Cin zarafin da Babban Jami’an tsaro (CSO) na Gwamnan Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba ya yi ga wakilin Talabijin NTA da ke Damaturu, Babagana Kolo a harabar Majalisar Dokokin Yobe da ke Damaturu a ranar Alhamis ya tada ƙura.
Lamarin ya faru ne yayin da wasu ’yan jarida ke jiran a shigar da su cikin zauren domin su bayar da rahoto kan gabatar da kasafin kuɗin 2026 da Gwamna Mai Mala Buni ya yi a gaban Majalisar Dokokin.
Shaidu sun ce Babban Jami’in tsaro (CSO) na fadar gwamnatin Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba, ya afka wa Kolo ya buge shi a fuska, lamarin da ya yi sanadiyyar raunuka a bakinsa da wasu ɓangarorin jikinsa.
An ruwaito cewa, lamarin ya kawo cikas ga yadda kafofin yaɗa labarai ke yaɗa labaran taron yayin da ‘yan jarida ke barazanar ƙauracewa gabatar da kasafin kuɗin.
Sai da Kwamishinan Yaɗa labarai, Alhaji Abdullahi Bego ya sa baki kafin ‘yan jaridar su ci gaba da ayyukansu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin ƙasa da ƙasa da shari’a ya jaddada muhimmancin kara karfafa dangantakar da ke tsakanin Tehran da Riyadh, yana mai cewa ci gaban kyakkyawar alaƙa tsakanin Tehran da Riyadh ba wai kawai yana da amfani ga ɓangarorin biyu ba ne, har ma zai kara karfafa zaman lafiya a yankin da ma a duniya.
Kazem Gharibabadi ya yi wannan furuci ne bayan ziyarar da ya kai Saudiyya da nufin fadada haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin manyan ƙasashen biyu.
Mataimakin ministan harkokin wajen ya jaddada cewa Iran da Saudiyya, waɗanda ke da alaƙa ta tarihi suna da kyakkyawan matsayi don yin hidima ga al’ummarsu da kuma taka domin ci gaban zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya.
Gharibabadi ya yi cikakken bayani game da ganawarsa da Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Saudiyya, Abdulrahman al Rassi.
Ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa a mataki na yankin da kuma na ƙasa da ƙasa.
Jami’an sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan ƙarfafa muhimmiyar rawar da Ƙungiyar Haɗin Kan Musulmi (OIC) ke takawa.
Gharibabadi ya ce ya jaddada bukatar da ke akwai ga OIC ta taka muhimmiyar rawa wajen magance muhimman batutuwa, ciki har da yin Allah wadai da laifukan mamayar da Isra’ila ta yi a Gaza da kuma cin zarafin da take yi a yankin, tare da fadada hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci