China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump
Published: 5th, November 2025 GMT
China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci.
A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana mai gargadin cewa Amurka za ta iya tura sojoji idan gwamnatin Najeriya ta gaza dakatar da abin da ya bayyana a matsayin ta’addacin masu kaifin kishin islama.
Ya kuma sanar da cewa za a saka Najeriya cikin jerin “kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.” ke sa wa ido.
Hukumomin Najeriya dai sun yi watsi da wadannan zarge-zargen, suna bayyana su a matsayin marasa tushe a game da gaskiyar lamarin kasar.
Da take mayar da martani ga tashin hankalin, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China Mao Ning ta ce Beijing zata tsaya tsayin daka tare da Abuja.
Ta kara da cewa “China tana adawa da duk wata kasa da ke amfani da addini ko hakkin dan adam a matsayin hujja don tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe ko kuma yi musu barazana da takunkumi ko karfi,” in ji Mao.
Ta kara da cewa China tana goyon bayan gwamnatin Najeriya gaba daya wajen samar da ci gaba”.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila November 5, 2025 Shugaban Najeriya Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU November 5, 2025 Kakakin Dakarun IRGC Ya Ce; Ko Kadan Amurka Ba Abar Amincewa Ba Ce November 4, 2025 Admiral Sayyari Ya Ce: Isra’ila Ba Ta Kai Matsayin Da Zata Yaki Iran Ba November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka
Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da cewa, Iran ta gudanar da yakin kwanaki goma sha biyu da wannan gwamnati mai wuce gona da iri, kuma ta hana ta ci gaba da mummunar manufarta ta mamaya a yankin.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al- Jazeera, Araqchi ya yi nuni da cewa: Gwamnatin masu wuce gona da iri ta yi kokarin fadada yakin zuwa yankin ta hanyar kai hari kan cibiyoyin man fetur na Iran, amma Iran ta yi nasarar shawo kan yakin kuma ta hana aukuwan hakan.”
Yayin da yake fayyace shirye-shiryen Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tattaunawa don kawar da damuwar da ake da ita game da shirin makamashin nukiliyarta na zaman lafiya, Ministan Harkokin Wajen ya jaddada cewa: “Sun shirya wa duk wani abu da zai faru kuma suna tsammanin duk wani hali mai tsauri daga ‘yan sahayoniyya.” Ya bayyana cewa Iran ta samu kwarewa mai yawa daga yakin da ta yi kwanan nan kuma ta samu damar gwada makamai masu linzaminta a wannan yaƙi na gaske.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani November 2, 2025 Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci