Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i
Published: 6th, November 2025 GMT
Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta amince da kudirin da ke kayyade hukuncin daurin shekaru 14 ga malamai da aka samu da laifin cin zarafin dalibai mata a manyan makarantu. Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke ci gaba da cewa, malamai suna amfani da damar dalibai masu neman maki ko wata alfarma sai su yi lalata da su – wannan matsalar ta tabbata a wani bincike da aka yi a jami’o’in Nijeriya tsawon shekaru, ciki har da binciken sirri na 2019 mai taken “Lalata don samun maki”, wanda ya fallasa cin zarafin da ake yi a wasu jami’o’i.
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai
Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA