Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan
Published: 7th, November 2025 GMT
Jami’i a Asusun yara na MDD y ace; Daga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu Yahudawa ‘yan share wuri zauna da sojojin HKI sun kashe kananan yaran Falasinawa 47,tare da yin gargadi akan hatsari dake tattare da hakan.
Manaja mai kula da yanayi na musamman a karkashin Asusun kananan yaran da MDD Recardo Peres ya ce; “Yan share wuri zauna da sojojin HKI sun kashe Kananan yaran Falasdinawa 47 a yammacin kogin Jordan da birnin Kudus tun daga watan Oktoba na 2023.
Haka nan kuma ya ce; Bayan abinda ya faru na barnar yakin tsawon shekaru biyu a Gaza, da tsagaita wutar da ake ketawa da kuma kashe yara a cikin sa’o’i kadan da su ka gabata, bai kamata a bar yammacin Kogin Jordan ya zama wani wajen tayar da hargitsi ba.
Haka nan kuma ya ce; Abinda yake faruwa a yammacin Kogin Jordan yana da hatsari sosai, domin yara suna mutuwa tun farkon fara yaki, don haka ya zama wajibi a kawo karshen hakan da gaggawa.
YAmmacin kogin Jordan dai yana fuskantar tashe-tashen hankula saboda hare-haren sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Da Kuma yahudawa ‘yan share wuri zauna.
A wani labarin daga Gaza, babban Darakta na Ofishin Yada Labarai na Gwamnati Dr. Ismail al-Thawabta, ya yi gargadin game da wani bala’i na jin kai da ke tafe yayin da hunturu ke gabatowa, ganin yadda Isra’ila ke ci gaba da hana shigar da tanti, da iskar gas zuwa yankin Gaza, duk da yawan lalata gidaje da matsugunan fararen hula.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon November 7, 2025 Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza November 7, 2025 Falasdinawa Miliyan 1.5 Ne Ke Cikin Mawuyacin Hali November 7, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya November 7, 2025 Karuwar Matsalar Jin Kai Mafi Girma A Duniya A Sudan Saboda Ci Gaba Da Masifar Yaki A Kasar November 7, 2025 An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jinin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar HDL Da Taimakon Rundunar RSF
Jakadan Saudan a MDD Hassan Hamid ya bayyana cewa; KAsarta tana yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kara matsin lamba akan HDL wacce take bai wa rundunar RSF makamai da sauran kayan soja.
Hamid wanda ya gabatar da taron manema labaru ya ce: ” Afili yake cewa daga ina ne rundunar RSF take samun makamai,abin takaici kuwa ba daga ko’ina ba ne sai HDL.
Jakadan na kasar Sudan a MDD ya yi kira da dakatar da bai wa wannan kungiyar ta ‘yan ta’adda makamai, ba tare da bata lokaci ba.
A can kasar Sudan ana ci gaba da fadace-fadace musamman a yankin Darfur.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta MDD ta fitar da bayanin dake cewa; ta sami rahotanni masu tayar da hankali, da su ka hada da yi wa mutane kisan gilla.
A baya sojojin kasar Sudan sun zargi rundunar kai daukin gaggawa ta RSF tana samun taimako daga HDL da makamai da kuma ‘yan ina da yaki daga kasashen Chadi, Libya, Kenya da Somaliya.
Daga cikin laifukan da ake zargin rundunar ta “Kai Daukin Gaggawa” da aikatawa da akwai cin zarfin mata da yi wa fararen hula kisan kiyashi sannan da wawason dukiyar mutane.
A ranar 26 ga watan Oktoba ne dai mayakan rundunar kai daukin gaggawar su ka kutsa cikin birnin Al-fasha, Babbar cibiyar yankin Darfur.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa November 5, 2025 Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci