Najeriya: Ta Sake Jaddada Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar
Published: 6th, November 2025 GMT
Gwamnatin Najeriya ta jaddada matsayinta na yin watsi da ayyata a matsayin kasa mai take hakkokin addinai da Amurka ta yi.
Da yake kare tarihin Najeriya, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce “barazanar Trump na ɗaukar matakin soja ba ta da tushe kuma hakan yana a matsayin kawar da ido ne daga ƙalubalen tsaro masu sarkakiya da Najeriya ke fuskanta,” ya ƙara da cewa “duk wani labari da ke nuna cewa Najeriya ta gaza ɗaukar mataki kan hare-haren da ake kai wa mabiya addini ya dogara ne akan bayanan ƙarya ko maganganu marasa tushe.
A ranar Litinin, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Olufemi Oluwedi, ya bayyana cewa “Najeriya tana fuskantar ta’addanci, ba kai hari ko cin motuncin Kiristoci ba,” kuma “shugabancin Najeriya yana maraba da taimakon Amurka wajen yaƙi da ta’addanci matuƙar tana mutunta haƙƙinta na yankuna.”
Idris ya ƙara da cewa gwamnatinsu ta samu ci gaba mai yawa a yaƙi da ta’addanci tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023, yana mai cewa “kofar gwamnatin Najeriya ta kasance a buɗe kuma tana son yin aiki kafada da kafada da gwamnatin Amurka da sauran ƙasashe da abokan hulɗa don cimma burin kawar da ta’addanci gaba ɗaya a ƙasar Najeriya.”
Idris ya jaddada cewa “ta’addanci ya shafi Kiristoci da Musulmai,” kuma gwamnati ta kuduri aniyar kawo ƙarshen ayyukan masu tsattsauran ra’ayi ta hanyar ɗaukar matakan soja, haɗin gwiwa a yanki, da tattaunawa da abokan hulɗa na duniya.
A makon da ya gabata, Shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da Najeriya cikin jerin ƙasashen da Amurka ta ce suna take ‘yancin addini. A ranar Asabar, ya ce ya umarci Ma’aikatar Tsaro da ta shirya don yiwuwar ɗaukar matakin soja cikin gaggawa idan Najeriya ba ta ɗauki mataki mai tsauri kan kisan Kiristoci ba. Matakin da Washington ta ɗauka ya kawo cikas ga dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Najeriya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume
Ya ce, “Wannan ba yana nufin ba a kashe Kiristoci ba ne.” Abin da muke faɗa shi ne, ba Kiristoci kaɗai ake kashewa ba – ana kashe Musulmai ma,”
“Addinan biyu sun tabbatar da hakan, akwai kashe-kashen rayuka da yawa da ke faruwa a Nijeriya tsawon shekaru 16 da suka gabata da kuma fiye da haka daga rikicin Boko Haram a 2009. Babu wanda zai iya musanta hakan.
“Amma a ce kawai ana kai wa Kiristoci hari ya dogara ne da inda abin ya faru. Idan ya faru a yankin da Kiristoci suka mamaye, a zahiri Kiristoci ne za su kasance waɗanda abin ya shafa kamar yadda yake a yanzu a Benuwe da Filato.
“Idan ya faru a yankin da Musulmai suka mamaye, ya danganta da irin abin da ke faruwa a can, waɗanda abin zai shafa a zahiri Musulmai ne.
“Idan aka kai hari a coci, waɗanda abin zai shafa za su zama Kiristoci, haka idan a masallaci ne, Musulmai ne za su kasance waɗanda abin ya shafa. Wannan shine gaskiyar magana,” in ji Sanata Ndume.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA