Aminiya:
2025-11-07@16:56:18 GMT

Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa

Published: 7th, November 2025 GMT

Wata kotu a Ƙasar Jamus ta yanke wa wani ma’aikacin jinya hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same shi da laifin kashe marasa lafiya 10 da kuma yunƙurin kashe ƙarin wasu 27 ta hanyar yi musu allurar guba.

Kotun da ke birnin Aachen a yammacin Jamus, ta tabbatar da cewa mutumin mai shekaru 44 ya aikata laifukan ne tsakanin watan Disamban 2023 zuwa Mayun 2024 a asibitin Wuerselen.

Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia

Kotun ta bayyana cewa laifin da ya aikata babban laifi ne, wanda zai hana shi samun ’yanci bayan shekaru 15 kamar yadda ake yadda a irin waɗannan shari’o’in.

Ba a bayyana sunan mutumin ba, amma masu gabatar da ƙara sun ce yana “wasa da rayuwar marasa lafiyar” da yake kula da su.

Lauyansa ya roƙi kotu ta wanke shi lokacin da aka fara shari’ar a watan Maris.

Masu gabatar da ƙara sun ce mutumin yana yi wa marasa lafiya, waɗanda mafi yawansu tsofaffi ne, allurar magunguna masu sa barci da rage zafi don rage wahalar aikinsa a lokacin dare.

Sun kuma bayyana cewa mutumin yana da matsalar halayya, ba ya nuna tausayawa ga marasa lafiya, kuma bai nuna nadama ba a lokacin shari’ar.

Haka kuma, sun ce yana amfani da morphine da midazolam, wani magani da ake amfani da shi a wasu lokuta wajen aiwatar da hukuncin kisa a Amurka.

An kuma sake zarginsa da yin aiki ba tare da bin ƙa’ida ba, da kuma rashin nuna ƙwazo a aikinsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Allura Ma aikacin Jinya marasa lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirinsa na ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 1.150, don cike gibin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025.

Buƙatar na kunshe ne cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata.

An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump HOTUNA: Mun kori jami’ai fiye da 100 cikin shekara guda — DSS

A cikin wasiƙar, Shugaba Tinubu ya ce za a samo bashin ne daga kasuwar bayar da lamuni ta cikin gida.

Ya ce buƙatar karbo bashin ta zama dole ne sakamakon ƙarin girman kasafin kuɗin shekarar 2025. Shugaban ya kuma ce an gabatar da buƙatar ne bisa tanadin Sashe na 44 (1) da (2) na Dokar Ƙarfafa Tattalin Arziki.

Bayan karanta wasiƙar, Akpabio ya mika buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da Na Waje domin ci gaba da nazari, tare da umarnin su kawo rahoto cikin mako guda.

Hakan dai na zuwa ne kwanaki shida kacal bayan Majalisar ta amince da buƙatar Tinubu ta karbo bashin dala biliyan 2.3 daga ketare, wanda shi ma za a yi amfani da shi don cike gibin kasafin kuɗin na 2025.

A cikin watanni huɗu da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kuma nemi amincewa da lamunin Dala miliyan 21.5 da Yen biliyan 15, tare da tallafin euro miliyan 65, a matsayin wani ɓangare na shirin lamunin waje na gwamnatin tarayya na shekarar 2025–2026.

Duk da ikirarin gwamnatin Tinubu na cewa samun kuɗaɗen shiga ya ƙaru tun bayan hawansa mulki, bashi ya ci gaba da zama hanyar cike gibin kasafin kuɗi.

A cewar Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya (DMO), daga ranar 31 ga Disamba, 2024, jimillar bashin da Najeriya ke da shi ya kai naira tiriliyan 144.7 (kimanin dala biliyan 94.2).

Ƙaruwar bashin ta haifar da ƙarin kuɗaden da ake kashewa wajen biyan bashi. A shekarar 2023, Najeriya ta kashe naira tiriliyan 7.8 wajen biyan bashi, ƙari da kaso 121 cikin 100 idan aka kwatanta da naira tiriliyan 3.52 a shekarar da ta gabata.

A wata hira da manema labarai a watan Disamban bara, Shugaba Tinubu ya kare bukatarsa ta ciyo bashi, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne ba don jefa ’yan Najeriya cikin wahala ba, sai don cika burinsa na inganta gine-gine da ababen more rayuwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karuwar Matsalar Jin Kai Mafi Girma A Duniya A Sudan Saboda Ci Gaba Da Masifar Yaki A Kasar
  • An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
  • Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
  • An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita
  • Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai
  • Za A Gudanar Da Taron Masana Harkokin Yada Labarai Karo Na 2 A Kano
  • Kwamishinan Kano Na Ziyarar Tabbatar Da Zaman Lafiya A Wannan Kaka
  • Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150
  • An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump