Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe
Published: 7th, November 2025 GMT
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawat 1 a garin Talasse, karamar hukumar Balanga.
Aikin, wanda aka kulla ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), Bankin Duniya, da kamfanin MIDS Dynamics, na da aniyar samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba ga sama da gidaje 8,000 a Talasse da kauyuka makwabta, idan aka kammala shi cikin watanni huɗu.
A wajen bikin kaddamar da aikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana shi a matsayin muhimmin ci gaba a shirin gwamnatinsa na bunƙasa makamashi mai tsabta, araha da kuma dorewa.
“Wannan aiki ba kawai zai ba da haske ga gidaje ba ne kawai, zai ƙarfafa kasuwanci, ya samar da ayyukan yi, kuma ya kawo ci gaban tattalin arziki a yankin,” in ji Gwamnan.
Ya ƙara da cewa aikin ya nuna nasarar haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu wajen ci gaban fannin makamashi, tare da yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa gyare-gyaren da yake kawo wa fannin wutar lantarki, musamman Dokar Wuta ta 2023, wadda ta bai wa jihohi damar tsara hanyoyin samar da makamashinsu.
Shugaban REA, Injiniya Abba Aliyu, ya jinjina wa Gwamna Inuwa bisa hangen nesa da jajircewarsa wajen inganta makamashi a jihar, inda ya ce hukumar na shirin aiwatar da ƙarin ayyukan sola a ƙananan hukumomi 10 na jihar.
A nasa bangaren, Shugaban MIDS Dynamics, Injiniya Halis Mohammed, ya bayyana Gombe a matsayin jiha ta farko a Najeriya da ta bayar da kuɗin haɗin gwiwa don irin wannan aiki, kuma jagora a sauyin makamashi.
Shugabannin yankin, ciki har da Bala Waja, Alhaji Mohammed Danjuma Mohammed, da Dan Majalisa Musa Buba, sun gode wa Gwamnan bisa cika alkawarin da ya ɗauka, tare da alƙawarin kare aikin daga lalacewa da satar kayan aiki.
“Mun daɗe muna jiran wannan rana. Yanzu haske ya dawo cikin ƙasar Waja,” in ji ɗaya daga cikin shugabannin yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Lantarki wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICEF
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICE
Daga Abdullahi Shettima.
Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ga yara kanana (RUTF) wanda hakan ya zama wani muhimmin mataki wajen yakar karancin abinci mai gina jiki tsakanin yara.
Da take jawabi yayin wani taron hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kaduna, wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta bayyana yadda jihar Kaduna ta nuna gagarumar jajircewa a bangaren kiwon lafiya tare da samar da walwalar yara da cika alkawuran kuɗin haɗin gwiwa akai-akai.
Tace “Jihar Kaduna ta zama abin koyi ga sauran jihohi. Yadda gwamnati ta rungumi shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ( RUTF) da sauri kuma ta fara aiwatar da shi na nuna cikakkiyar niyya wajen kare rayuwar yara da tabbatar da cewa babu wani yaro da zai ci gaba da fama da rashin abinci mai gina jiki,”
Taron wanda aka gudanar da shi a fadar gwamnatin jihar Kaduna, ya zama abin tarihi a dangantakar hadin gwiwar da ke tsakanin UNICEF da gwamnatin jihar Kaduna wajen inganta lafiya da walwalar yara.
Gwamna Uba Sani ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gina kan wannan nasara, inda ya bayyana shirin RUTF a matsayin wani muhimmin ɓangare na dabarar gwamnatin sa wajen yakar rashin abinci mai gina jiki da inganta ci gaban jama’a baki ɗaya.
“Kaddamar da rabon abincin RUTF a fadin jihar Kaduna wani babban mataki ne na kawo ƙarshen cutar karancin abinci mai gina jiki,”
“Mun kuduri aniyar cewa babu wani yaro da za a bar shi a baya wajen yaƙar yunwa, rashin lafiya, da kuma samar da makoma mai kyau.” inji gwamna Uba Sani
Gwamnan ya kuma godewa UNICEF bisa wannan haɗin gwiwar da ke samar da sauye-sauye masu amfani a fannoni kamar su lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi, da tsaftar ruwa da muhalli.
Ya kara da cewa shiga jihar Kaduna cikin muhimman shirye-shirye irin su RUTF da ASWA III wanda Kaduna ita kaɗai ce ta shiga cikinsa a Nijeriya na nuna hangen nesan gwamnatinsa na gina tsarin da ke tallafa wa marasa ƙarfi a fadin jihar baki daya.