Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani
Published: 27th, July 2025 GMT
Daga ranar 24 ga wata, zuwa jiya Asabar 26 ga wata, an gudanar da babban taron kasa da kasa, dangane da fasahar rage asarar hatsi a birnin Jinan na kasar Sin, inda a wajen taron aka sanar da sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin takaita asarar hatsi.
An bayyana cewa, a bangaren asarar hatsi da a kan samu yayin da ake girbin hatsi da injuna, yawan asarar alkama, da shinkafa, da masara, da aka samu a kasar Sin a shekarar 2024, ya kai kaso 0.
Kana ta fuskar tinkarar bala’i, da magance tafka hasara sakamakon hakan, kasar Sin ta riga ta gina ingatattun filayen gona da fadinsu ya kai muraba’in kilomita dubu 667. Kana kasar ta dauki gagarumin mataki na haka magudanar ruwa cikin gonaki, ta yadda aka tabbatar da ingancin aikin ban ruwa, da fitar da ruwa a lokacin ambaliya, a cikin fiye da rabin gonakin kasar. Ban da haka, kasar ta karfafa yin gargadin yiwuwar abkuwar cututtukan da suka shafi hatsi, da bala’in kwari, ta yadda ake samu damar rage asarar hatsi da yawansa ya kai fiye da kilo biliyan 140 a duk shekara. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: asarar hatsi
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar
A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, bisa hadarin jirgin saman fasinja da ya auku a kasar, wanda ya haddasa rasa rayuka da dama.
Kafar dillancin labarai ta “The Russia Today”, ta hakaito kwamitin binciken hadarin na cewa, dukkanin mutanen dake cikin jirgin saman mai lamba An-24 da ya yi hadari a yau Alhamis a yankin Amur na kasar Rasha sun rasu. An ce, jirgin na dauke da fasinjoji 43, da kuma matuka da masu bayar da hidima 6. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp