Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Published: 8th, November 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025
Manyan Labarai Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10 November 8, 2025
Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta buɗe kofofin tattaunawa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, dangane da barazanar kasar ta kaddamar da yaki a Najeriya.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, Ministan ya ce gwamnatinsu ba ta son ƙara yin yamadidi da maganar.
An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa“Babban nauyin da ke kanmu a matsayin gwamnati shi ne tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar mataki a kan duk wata damuwa ta gaskiya da ke da alaƙa da tsaron ’yan ƙasa.
“Amma ba ma cikin yanayin firgici. Muna mayar da martani cikin natsuwa, hankali, da kuma la’akari da muradun ƙasarmu, tare da duba damuwar da ke cikin gida da waje dangane da halin da ake ciki. Amma zan sake jaddadawa, Najeriya ƙasa ce mai ba da ’yancin yin addinai,” in ji ministan.
Ya kuma ce gwamnati na mayar da martani kan waɗannan batutuwa ta hanyar kiyaye mutunci da darajar ƙasar, da kuma haɗin gwiwa da kowa, ciki har da ƙasashen duniya, don magance wannan matsala.
“Muna da iyakoki masu sauƙin shigowa, shi ya sa muke da fahimtar juna da makotanmu. Haka kuma muna da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, kuma Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa. Mun fara magana da gwamnatin Amurka. Hanyoyin sadarwar mu a bude suke. Muna so a warware wannan matsala ta hanyar diflomasiyya.
“Baya ga siyasar lamarin, muna ɗaukar batun da muhimmanci. Amma ina so in ƙara jaddada cewa gwamnati, tun kafin abubuwan da suka faru a kwanakin baya, ta jajirce matuƙa wajen tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce amintacciya ga kowa.
“Shin akwai matsalolin tsaro a ƙasa? Eh, akwai. Shin ana kashe mutane a wasu sassan ƙasa? Eh. Amma shin gwamnati na yin wani abu don dakile hakan? Eh, tabbas akwai. Shin gwamnati na mayar da martani? Eh, tana yi. Amma ana yin hakan cikin cikakken hanyoyin da suka dace, tare da kiyaye daidaito da ake buƙata don fuskantar waɗannan matsaloli kai tsaye,” in ji shi.