Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba
Published: 27th, September 2025 GMT
Wani ɗalibi mai suna Ogbeche, ya kashe malaminsa Oshen, a makarantar sakandire da ke garin Ugboro, da ke Ƙaramar Hukumar Bekwarra a Jihar Kuros Riba.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya yi ƙoƙarin raba faɗa tsakanin Ogbeche da wani ɗalibi.
Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Matatar Ɗangote ta dakatar da sayar da fetur a farashin NairaSai dai a fusace, ɗalibin ya fisge taɓarya daga hannun wata mata, ya buga wa malamin a kai, wanda hakan ya sa ya faɗi sumamme.
Duk da garzayawa da shi da aka yi zuwa asibiti, likitoci sun tabbatar da mutuwarsa.
Wata ganau mai suna Lizzy ta ce: “Malamin kawai yaje rabon faɗa ne, amma Ogbeche ya fusata ya ɗauki taɓarya ya buga masa a kai, nan take ya faɗi.”
Al’ummar yankin sun nuna ɓacin ransu, inda suka ce abin da ɗalibin ya aikata ba abin yadda ba ne, domin ya hallaka malaminsa.
Yanzu haka, rundunar ’yan sandan jihar, ta kama Ogbeche, inda ake masa tambayoyi kafin a miƙa shi zuwa hedikwatar rundunar domin ci gaba da bincike.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.
Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta.
El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin NijeriyaBayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya.
Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin cewa matar ta kashe yarinyar ce a gidanta bayan ta je har makarantarsu ta ɗauko ta ba tare da izinin mahaifiyarta ba.
Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce an kai gawar yarinyar ɗakin ajiye gawa domin bai wa likitoci damar kammala bincikensu na kimiyya gabanin soma nasu binciken.
“Mun ziyarci wurin da abin ya faru, mun ɗauki hotuna, kuma an garzaya da su asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu.”