Aminiya:
2025-11-09@11:26:42 GMT

’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra

Published: 9th, November 2025 GMT

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana.

Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin nan kafin kowa ya ankara. Daga nan suka tsere da motarsu ba tare da sun cutar da wani ba.”

Wannan lamari ya jefa masu jefa ƙuri’a cikin firgici da tsoro, inda wasu suka bayyana damuwa kan abin da ka iya biyo baya kafin a kammala zaɓen.

Wani mazaunin yankin da ke wurin a lokacin faruwar lamarin ya ce: “Abin ya firgita mu. Ana zaune lafiya kawai sai a ji an kashe mutum haka. Wannan abu ya girgiza mu sosai domin ba a taɓa samun matsala irin wannan a  mazabar nan ba.”

Shi ma wani mai suna Odemenna, wanda ya kasance a wurin, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin gudanar da bincike da kuma neman waɗanda suka aikata wannan aika-aika.

A cewar wani mazaunin yankin, Chukwudi Chinanso: “Maharan sun kai harin ne kan kansilan, kuma sun yi sa’ar tarar da shi ne lokacin da ya zo jefa ƙuri’a. Da nan suka harbe shi suka gudu.”

Haka zalika, wata mata mai suna Joyce Okoro ta shaida cewa: “Wasu matasa ɗauke da muggan makamai sun zo mazabar mu suka harbe kansilan sannan suka tsere.”

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin rikicin siyasa ne ya haddasa kisan, kasancewar Nze Ala Kuru Orji ɗaya ne daga cikin shugabannin jam’iyyar APGA a mazabar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’ansu sun shiga bincike domin cafke masu hannu a cikin wannan ɗanyen aiki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jihar Anambra Zaɓen Gwamna

এছাড়াও পড়ুন:

Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa

Kwamishinan lafiya na Jihar Adamawa, Dokta Felix Tangwami ya bayyana cewa, cutar kwalara a Ƙaramar hukumar Mubi ta yi sanadin mutuwar mutane 10, inda ya buƙaci mazauna yankin da su kula da tsaftar jikinsu.

Da yake yi wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) bayani a Yola ranar Laraba, Tangwami ya ce marasa lafiyan sun mutu ne a gida maimakon a cibiyoyin lafiya.

Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita

Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ɗauki matakin gaggawa don daƙile ɓarkewar cutar.

“Tun daga farko, mun ɗauki matakin gaggawa a kan lamarin, kasancewar mu a can, kuma ba za a iya musanta hakan ba,” in ji shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, waɗanda suka ziyarci cibiyoyin kiwon lafiya sun samu kulawa, inda aka kwantar da majinyata 25 a ranar Talata 4 ga watan Nuwamba, yayin da wasu da dama kuma an sallame su tare da wayar da su kan harkokin tsafta.

Ya bayyana cewa, an tura jami’an kula da cututtuka na jihar, da Daraktan kula da cututtuka a Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko, da masu aikin sa-kai zuwa Mubi domin gudanar da ayyuka da kuma wayar da kan jama’a.

Sun kuma gano waɗanda abin ya shafa a cikin unguwanni don tabbatar da sun samu kulawar lafiya.

Tangwami ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da su goyi bayan ƙoƙarin gwamnati ta hanyar ƙarfafa gwiwar mazauna yankin da su gaggauta neman magani a cibiyoyin lafiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
  • Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu
  • Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato
  • An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa
  • An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi
  • Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan
  • Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
  • An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita