An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno
Published: 23rd, September 2025 GMT
Wata Kotun Soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, Jihar Borno.
Kotun sojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Mohammed Abdullahi, ta bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka ɗaure mutum ɗaya shekaru 15 a gidan yari.
Sojojin da abin ya shafa sun haɗa da Raphael Ameh da Ejiga Musa masu muƙamin sajan, da kuma Patrick Ocheje mai muƙamin kofura.
Binciken kotun ya nuna cewa Ameh ya karɓi sama da ₦500,000 daga harƙallar sayar da harsasai kafin daga bisani a kama shi yana ƙoƙarin sayar da wasu ƙarin makaman.
Da yake yanke hukunci, Janar Abdullahi ya bayyana su a matsayin “ƙwayaye bara-gurbi” da suka ci amanar rundunar soji, suka karya ƙa’idar ladabi da biyayya, tare da wulaƙanta mutuncin da ake tsammani daga jami’an soja a yaƙin da ake yi da ta’addanci.
Bayanai sun ce wannan hukuncin na zuwa ne bayan amincewar su kan aikata laifuffukan da suka haɗa da “sata da cinikin makamai ba bisa ka’ida ba, da taimaka wa maƙiya” wanda duka laifuka ne ƙarƙashin dokar sojojin Najeriya.
Kotun ta bayyana cewa “irin wannan safarar da ba bisa ƙa’ida ba na zama haɗari ga sojoji da ayyukansu, da kuma tsaron ƙasa, don haka yana nufin taimaka wa maƙiyan ƙasar.”
Shugaban Kotun, Brigadier Janar Abdullahi, ya ce waɗannan laifuka da sojojin suka aikata ba matsala ce kawai ta karya doka ba, har ma da cin amana, da martabar da ake sa ran sojoji su riƙe.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta lamunci irin waɗannan rashin ɗa’a da halayen damfara ko rashin ƙwarewa ba.
Babu shakka Jihar Borno ce cibiyar rikicin Boko Haram a Najeriya wadda ta kwashe kimanin shekara 15 tana fama da shi, lamarin da ya laƙume rayukan dubban mutane da haifar da matsalar jin-ƙai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Borno
এছাড়াও পড়ুন:
An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai
Majalisar Tarayya ta amince da hukuncin cin sarƙa ga duk wani malami da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a makarantu a faɗin ƙasar nan.
Hakan ya biyo bayan amincewar majalisar da Dokar Hana Lalata da Dalibai ta 2025 (HB.1597), bayan tsallake karatu na uku a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai a ranar Laraba.
Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a JosA ƙunshin bayanan da dokar, za a iya yanke wa duk wanda ya saɓa mata hukuncin ɗaurin shekara 14 ko shekara biyar mafi ƙaranci ba tare da zaɓin biyan tara ba.
Laifukan da dokar ta bayyana a matsayin cin zarafi sun haɗa da yin jima’i ko neman wata alfarma daga ɗalibai a madadin jima’i, barazana, ko tozartarwa da ɗaga hankali a wajen karatu, ko taɓawa ko rungumar jiki.
Haka kuma dokar ta haɗa da aika saƙonnin batsa, hotuna ko bidiyo, ko barkwanci ko magana mai ɗauke da cin zarafi kan jikin ɗalibi, da kuma bibiya da sa ido mai tsanani.
Sabuwar dokar, wadda ke jiran sahalewar shugaban ƙasa kafin ta fara aiki, ta bai wa waɗanda abin ya shafa damar shigar da ƙarar malamin da ya aikata laifin na cin amana.
Haka kuma dokar ta wajabta wa duk makarantu na gaba da sakandare su kafa kwamitin musamman mai zaman kansa domin kula da korafe-korafe da suka shafi cin zarafi, a bisa tsarin doka.
Dokar ta ce ba za a ɗauki yarda daga ɗalibi a matsayin hujja ta kare kai ba, sai idan ɓangarorin biyu sun yi aure bisa doka. Ta kuma bayyana cewa ba sai an tabbatar da niyyar cin zarafi ba kafin a samu hukunci.
Haka zalika, ta haramta wa makarantu gudanar da bincike na cikin gida idan an riga an kai ƙara kotu, inda ta ce har sai an gama shari’ar kafin su iya shiga tsakani.
Dokar ta kuma bai wa ɗalibai, ’yan uwa, wali ko lauya damar kai ƙara, tare da ba da damar miƙa rahoto ga rundunar ‘yan sanda ko ofishin Antoni-Janar, sannan a tura kwafin ƙarar ga kwamitin hana cin zarafi na makarantar da abin ya shafa.