Aminiya:
2025-11-05@12:02:02 GMT

Mamdani ya zama Musulmi na farko da ya zama magajin garin New York na Amurka

Published: 5th, November 2025 GMT

Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar, duk da suka daga Shugaba Donald Trump da ‘yan Republican, da wasu ‘yan Democrat masu matsakaicin ra’ayi.

Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump A jawabin nasararsa bayan doke tsohon Gwamna Andrew Cuomo, Mamdani ya ce yana da cikakken goyon baya daga jama’a, kuma ya bayyana kansa a matsayin wanda ke gaba da Trump. Ya ce, “A wannan lokaci na duhun siyasa, New York zai zama birni haske.” Ya ƙara da cewa, “Tare za mu kawo sauyi ga wannan zamani. Idan muka rungumi wannan sabuwar hanya ta jarumta maimakon mu gudu daga gare ta, za mu iya fuskantar mulkin masu kuɗi da na danniya da ƙarfin da suke tsoro, ba da sassaucin da suke nema ba.” Mamdani ya ci gaba da kalubalantar Trump kai tsaye: “Wannan ba kawai yadda za mu dakatar da Trump ba ne, har da wanda zai biyo bayansa. Don haka Donald Trump, tun da na san kana kallo, ina da kalmomi guda huɗu gare ka: Kara sauti.” Jawabinsa bai tsaya kan Trump kaɗai ba. Ya fara da ambaton Eugene Debs, wani ɗan gurguzu na ƙarni na 19 da 20, sannan ya yi alkawarin aiwatar da “tsarin da ya fi kowanne girma” don rage tsadar rayuwa a New York tun bayan zamanin Magajin Gari Fiorello LaGuardia kusan shekaru 100 da suka wuce. Mamdani ya doke Cuomo, wanda ya tsaya takara a matsayin ɗan mai zaman kansa bayan faduwa a zaɓen fidda gwani na Democrat a watan Yuni, da kusan maki 9. Dan takarar Republican Curtis Sliwa ya zo nesa da Mamdani. Magajin Gari Eric Adams, wanda ya tsaya takara a matsayin ɗan jam’iyya ta uku bayan nasararsa a 2021 a matsayin Democrat, ya janye a watan Satumba kuma ya goyi bayan Cuomo a watan da ya gabata. Wannan nasara ta Mamdani ta nuna yadda ya yi tasiri cikin siyasar New York cikin shekara guda, daga matsayin ɗan majalisar jiha da ba a san shi ba sosai, zuwa jagoran birni mafi girma a Amurka.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump

China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci.

A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana mai gargadin cewa Amurka za ta iya tura sojoji idan gwamnatin Najeriya ta gaza dakatar da abin da ya bayyana a matsayin ta’addacin masu kaifin kishin islama.

Ya kuma sanar da cewa za a saka Najeriya cikin jerin “kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.” ke sa wa ido.

Hukumomin Najeriya dai sun yi watsi da wadannan zarge-zargen, suna bayyana su a matsayin marasa tushe a game da gaskiyar lamarin kasar.

Da take mayar da martani ga tashin hankalin, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China Mao Ning ta ce Beijing zata tsaya tsayin daka tare da Abuja.

Ta kara da cewa “China tana adawa da duk wata kasa da ke amfani da addini ko hakkin dan adam a matsayin hujja don tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe ko kuma yi musu barazana da takunkumi ko karfi,” in ji Mao.

Ta kara da cewa China tana goyon bayan gwamnatin Najeriya gaba daya wajen samar da ci gaba”.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025  Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila November 5, 2025 Shugaban Najeriya Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU November 5, 2025 Kakakin Dakarun IRGC Ya Ce; Ko Kadan Amurka Ba Abar Amincewa Ba Ce November 4, 2025 Admiral Sayyari Ya Ce: Isra’ila Ba Ta Kai Matsayin Da Zata Yaki Iran Ba November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karon farko an zabi Musulmi magajin New York, birni mafi girma a Amurka
  • China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump
  • Musulmi na farko ya lashe zaɓen magajin garin New York a Amurka
  • An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla
  • Admiral Sayyari Ya Ce: Isra’ila Ba Ta Kai Matsayin Da Zata Yaki Iran Ba
  • KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICEF
  • Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?