Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta
Published: 8th, November 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: A bayyane yake cewa Amurka tana da hannu dumu-dumu wajen wuce gona da iri kan kasar Iran
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya mayar da martani ga amincewar da shugaban Amurka ya yi na daukar alhakin harin da sojojin Sahayoniyya suka kai wa Iran, yana mai cewa: “Tun daga farko a bayyane yake cewa Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran.
Baqa’i ya rubuta a shafinsa na X-Platform: “Shin kuna tuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 cewa: Amurka ba ta da hannu a harin da ‘yan Sahayoniyya suka kai wa Iran, kuma ya jaddada cewa wannan ‘aikin hadin gwiwa ne’ da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi kuma ‘ba su da hannu a hare-haren da aka kai wa Iran’?”
Ya ci gaba da cewa: “Wannan ikirarin karya ce karara, domin tun daga farko ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran. Yanzu shugaban Amurka ya yarda cewa shi ne ke da alhakin hakan, yana fallasa karyar sakataren harkokin wajensa kuma a zahiri ya yarda cewa Amurka ce ke da alhakin gudanar da wannan aikin tun daga farko.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran November 8, 2025 Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila November 8, 2025 Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025 Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon November 7, 2025 Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza November 7, 2025 Falasdinawa Miliyan 1.5 Ne Ke Cikin Mawuyacin Hali November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari
Iran ta sanar da yi wa ‘yan faransa nan guda biyu da take tsare saki bisa sharadi a zarginsu da akeyia da yi wa tsaron kasar Iran zagon kasa.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya fitar da bayanin sakin yana mai cewa na yi shi ne “bisa umarnin alkali.”
Ya kara da cewa za su ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar shari’a har sai an ci gaba da shari’a.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana mutanen biyu a matsayin Cécile Kohler da Jacques Paris, wadanda aka tsare a Iran bisa zargin leken asiri.
A halin yanzu suna Ofishin Jakadancin Faransa da ke Tehran.
A ranar 21 ga Oktoba, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Vahid Jalalzadeh ya sanar da cewa Mahdieh Esfandiari, wata ‘yar Iran da aka tsare ba bisa ka’ida ba a Faransa saboda wallafa sakon goyan bayan falasdinu a kafofin sada zumunta, an saka ta cikin shirin musayar fursunoni.
A ranar 22 ga Oktoba, Mista Baghai ya sanar da sakin Ms. Esfandiari bisa sharadi a cen faransa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Karon farko an zabi Musulmi magajin New York, birni mafi girma a Amurka November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci