Zulum ya bai wa hukumomin tsaro kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Borno
Published: 5th, November 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa hukumomin tsaro da rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Maiduguri.
Daga cikin motocin, an bai wa rundunar CJTF guda 30, jami’an tsaro 16, ƙungiyoyin tsaro 10, mafarauta shida, sannan aka bai wa hukumar NAPTIP guda ɗaya.
An raba motocin ne domin inganta sintiri da kai ɗaukin gaggawa, domin yaƙi da laifuka da barazanar tsaro irin su ’yan daba da sauran masu aikata laifi a Maiduguri da kewaye.
Wannan na cikin irin tallafin da Gwamna Zulum ke bayarwa don inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Yayin ƙaddamar da rabon, Gwamna Zulum ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ya ce: “Gwamnatinmu za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro dukkanin goyon bayan da ake buƙata don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Borno.”
Zulum ya kuma gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da dukkanin jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na wanzar zaman lafiya a jihar.
Taron rabon ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Dakta Umar Usman Kadafur, Sakataren Gwamnati Bukar Tijani.
Sauran sun haɗa da Kwamishinan ’Yan Sanda, Naziru Abdulmajid, Daraktan Hukumar Tsaro, Adamu Umar da sauransu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Tsaro jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta ayyana ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Wannan mataki da rundunar ta ɗauka na zuwa ne bayan zargin Sowore da yunƙurin ta da zaune tsaye da kawo hargitsi da sunan zanga-zanga a Jihar Legas.
Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar Nijeriya An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a TanzaniyaKwamishinan ‘yan sandan jihar, Olorundare Jimoh, ya bayyana cewa tun da fari rundunar ta gargaɗi Sowore kan kada ya jagoranci wata zanga-zanga da aka gudanar kan wani rusau da hukumomi suka gudanar a yankin Oworonshoki na jihar.
Sai dai rundunar ta bayyana cewa Sowore ya yi wa gargaɗin nata kunnen-uwar-shegu, inda ya shirya mutane suka fita tituna domin gudanar da zanga-zanga duk da cewa shi bai halarta ba.
Ana iya tuna cewa dai, Sowore, wanda shi ne jagoran “Take It Back Movement”, ya yi barazanar gudanar da zanga-zanga a makonnin baya domin nuna adawa da rusa gidajen da gwamnati ta yi da sunan shirin sabunta birni a Jihar Legas.