Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250 a Jami’ar Ilorin
Published: 15th, September 2025 GMT
Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.
An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin.
Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin.
Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.
Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar RuwaYa ce an riga an rattaba hannu kan yarjejeniya da Jami’ar Ilorin wadda ta ba wa masallacin damar mallaka da gudanar da ɗakin kwanan ɗaliban na tsawon shekaru 21 kafin a miƙa shi ga jami’ar.
Baya ga aikin ginin, Ɗangote ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira miliyan 5 a kowane wata domin kula da masallacin har sai an kammala aikin.
AbdulGafar ya ce wannan taimako zai rage nauyin kuɗin aikin, tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan masallacin.
Ya ƙara da cewa ɗakin kwanan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin wurin kwana ga ɗaliban jami’ar.
Shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa Ɗangote, sun bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi na yadda za a iya haɗa kai tsakanin cibiyoyin addini da ’yan kasuwa wajen ci-gaban al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɗakin kwanan ɗalibai Ɗangote Jami ar Ilorin
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.
Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp