Kwamishinan Habbaka kiyon Dabbobi na Jihar Kano, Dr. Aliyu Isa Aliyu, ya fara ziyarar wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Ajingi da Dawakin Tofa.

Ziyarar ta yi daidai da shirin gwamnati na kaucewa rikici, musamman sakamakon yuwuwar shigowar makiyaya daga Jamhuriyar Nijar cikin jihar.

A Ajingi, Dr. Aliyu ya jagoranci tawaga ta jami’an tsaro, ma’aikatan ma’aikatar da shugabannin kungiyoyin manoma da makiyaya, inda ya bukaci tattaunawa, fahimtar juna da zaman lafiya, domin kauce wa sabani.

Wakilin Hakimin yankin, Alhaji Abdulkadir Abdullahi, da shugaban karamar hukumar Dr. Abdulhadi Chula, sun yaba da wannan yunkuri tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kafa ma’aikatar da naɗa kwamishina mai nagarta.

A Dawakin Tofa kuwa, kwamishinan ya samu wakilcin Daraktan Gudanarwa, Yahya Sani Abbas, wanda ya tabbatar da cewa gwamnati tana da cikakkiyar niyyar tallafawa rayuwa da ayyukan manoma da makiyaya.

Shi ma, wakilin Hakimin yankin, Malam Muhammad Ubale, ya tabbatar da cikakken haɗin kai domin dorewar zaman lafiya.

Dr. Aliyu ya ce ma’aikatar za ta ci gaba da aiki domin inganta kiwon dabbobi na zamani, ciki har da inganta nau’in dabbobi da sarrafa madara da kiwon lafiya da rigakafin cututtuka da samar da dakunan gwaje-gwaje na zamani.

Khadijah Aliyu Kano

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gina Gadar Sama Da Ta Kasa A Mararraba

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce ta samu amincewar gwamnatin tarayya domin gina sabbin gada biyu na sama da kuma ta karkashin kasa (under-pass) a yankin Mararaba da ke Karamar Hukumar Karu.

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Abdullahi Sule kan Harkokin Jama’a, Mr. Peter Ahemba, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.

A cewar Ahemba, gwamnati za ta fara aikin kafin gwamnatin yanzu ta kai ga karewar wa’adinta a shekara ta 2027. Ya ce tun da dadewa Gwamna Abdullahi Sule ya ware kudaden aikin, kafin ma a kammala tsarinsa.

Ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2019, gwamnatin jihar ta kan ** tabbatar da ajiyar kuɗi kafin fara kowanne babban aiki**, saboda dorewa da tabbatar da kammalawa akan lokaci.

Ahemba ya ce gina wadannan flyovers da under-pass ya zama dole sakamakon cunkoson ababen hawa da ke addabar yankin Karu–Mararaba, musamman ga mazauna da direbobi da matafiya.

“Wannan aiki zai magance matsalar cunkoso, ya inganta tafiyar ababen hawa, tare da ƙara ingancin hanyoyi,” in ji shi.

Ya kara da cewa gwamna ya bai wa Hukumar Nasarawa State Urban Development Agency (NUDA) umarnin gudanar da bincike da tantance wuraren da suka fi dacewa domin gina wadannan ayyukan.

Mr. Ahemba ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar fara aikin, ta kuma kammala shi kafin karewar wa’adinta a 2027.

Aliyu Muraki, Lafia.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za A Gudanar Da Taron Masana Harkokin Yada Labarai Karo Na 2 A Kano
  • Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gina Gadar Sama Da Ta Kasa A Mararraba
  • Iravani: Kalaman Trump barazana ce ga zaman lafiyar duniya
  • 2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC
  • ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu
  • Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar
  • Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi
  • Marasa Lafiya A Nasarawa Sun Koka Game Da Yajin Aikin Likitoci
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna