Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar
Published: 4th, November 2025 GMT
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya gargaɗi Shugaban Amurka Donald Trump, kan kada ya ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya bayan zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar.
Mista Tuggar, wanda ya yi jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin tare da takwaransa na ƙasar Jamus, Johann wadephul, yana mai cewa Najeriya ƙasa ce mai bin doka da tsarin mulki, wadda ke tabbatar da cikakken ’yancin addini ga dukkan ’yan ƙasa.
“Kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin ƙasa sun haramta cin zarafin addini, kuma suna tabbatar da damar kowane ɗan ƙasa ya gudanar da addininsa cikin walwala da kwanciyar hankali,” in ji shi.
Ya ce babu yadda za a yi gwamnatin Najeriya ta goyi bayan duk wata hanya da za ta janyo cin zarafin mabiya wani addini, ko rikicin da zai haifar da tashin hankali irin wanda ya ruguza Sudan.
“Abin da muke so duniya ta fahimta shi ne, ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya. Ƙasarmu tana da yawan al’umma sama da miliyan 230, kuma ita ce ƙasa mafi girma ta dimokraɗiyya a Afirka,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ƙasashen waje za su bar ’yan Afirka su warware matsalolinsu da kansu, musamman Najeriya wadda ke cikin kwamitin tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, yaƙin da ake fafatawa a ƙasar Sudan da ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane tare da raba wasu miliyoyi da matsugunansu cikin shekaru biyu da suka gabata, inda yanzu haka yaƙin ya bazu zuwa wasu yankunan ƙasar, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar wani mummunan bala’i na jin kai.
Barazanar TrumpA ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Kiristocin Nijeriya suna fuskantar “barazanar gushewa” sakamakon kisan gillar da ake yi musu lamarin da ya ce shi ya sanya shi saka ƙasar a cikin ƙasashen da “ake matuƙar nuna damuwa a kansu.”
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
Trump ya ɗauki matakin ne duk kuwa da cewa kwanakin baya mai ba shi shawara kan harkokin Afirka, Mossad Bullos, ya yi watsi da iƙirarin da ke cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yusuf Tuggar
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya
Fadar Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan da wasu kwanaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya.
Mai ba wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin SudanA cewar Daniel Bwala, shugabannin biyu — Tinubu da Trump — sun yi tarayya da juna kan fahimta ta haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wata barazana ga bil’adama.
“A bayan nan Shugaba Trump ya taimaka wajen ba da izinin sayar wa Nijeriya makamai, kuma Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar yadda ya kamata wajen yaƙi da ta’addanci, kuma muna da sakamakon da za mu iya nunawa,” in ji Bwala.
Ya ƙara da cewa duk wani saɓanin fahimta kan ko ‘yan ta’adda a Nijeriya na kai hari ne ga Kiristoci kaɗai ko kuma mabiyan addinai daban-daban, “za a tattauna kuma a warware su” a yayin ganawar shugabannin biyu, wadda za ta gudana “ko dai a Fadar Shugaban Kasa ta Abuja, ko a Fadar White House da ke Washington.”
Sanarwar ta zo ne bayan barazanar Shugaba Trump ta kai farmaki a Nijeriya, inda ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta fara tsara yadda za a kai hari kan ƙasar, saboda abin da ya kira “kisan gillar da ake yi wa Kiristoci” a Nijeriya.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, Trump ya ce Amurka “a shirye take ta turo sojojinta da manyan makamai zuwa Nijeriya don kare Kiristoci,” yana mai cewa idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma “mai yiwuwa ta shiga ƙasar don kawar da ‘yan ta’adda masu zafin kishin Musulunci.”
Barazanar Trump ta jawo cece-kuce bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya, ba tare da ya bayyana takamaiman inda ya samo waɗannan alƙaluman ba.
Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai kiyaye dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.