Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata
Published: 8th, November 2025 GMT
Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida.
Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri.
Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — TinubuA yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu.
Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta tabbatar da wannan shiri.
Kakakin Majalisar, ya yaba da ƙoƙarin Uwargidan Gwamnan, inda ya ce wannan ziyarar “ta tarihi ce” kuma ya tabbatar da goyon bayan majalisar wajen ganin an aiwatar da ƙudirin.
Haka kuma, wakiliyar Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Miss Omowumi Gbamis, ta ce wannan doka zai taimaka wa mata su ci gaba da aiki lafiya tare da inganta lafiyar jarirai.
Kodinetan CS-SUNN a Gombe, Misis Comfort Mukollo, ta bayyana cewa suna aiki tare da UNICEF da ma’aikatun gwamnati don tallafa wa shirye-shiryen kula da abincin uwa da jariri tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin shayar da nono.
Daga cikin manyan jami’an da suka nuna goyon baya akwai Kwamishiniyar Harkokin Mata, Asma’u Mohammed Iganus, da Shugaban Kwamitin Lafiya na Majalisar, Siddi Buba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Haihuwa jarirai shayarwa Uwar Gidan Gwamna
এছাড়াও পড়ুন:
Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na shiyyar Abuja (AEDC) ya fara aikin rage ma’aikata kusan 800, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da fama da hauhawar farashi, tsadar rayuwa, da rashin tabbas wajen samun wutar lantarki.
Matakin korar wanda ta fara a ranar Laraba, ya biyo bayan watanni na sake fasalin cikin gida a kamfanin da ke ba da wutar lantarki ga Babban Birnin Tarayya Abuja da jihohin Kogi, Neja da Nasarawa.
Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-AllahMajiyoyi da dama da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa shugabannin kamfanin sun fara ne da shirin korar ma’aikata 1,800, kafin su rage adadin zuwa 800 bayan jerin tattaunawa masu zafi da Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa da Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki da Ƙungiyoyin Kwadago.
Wata majiya daga cikin ma’aikatan AEDC ta ce shugabannin kamfanin sun fara da shirin korar 1,800, amma sun rage zuwa 800 bayan matsin lamba daga ƙungiyoyin, waɗanda a farko suka dage cewa ba a kamata a kori kowa ba.
“Shugabanni sun so su kori 1,800, amma bayan matsin lamba, sun rage zuwa 800. Tun da farko kungiyoyin sun nemi kada a kori kowa,” in ji ma’aikacin da ya nemi a boye sunansa don kauce wa hukunta shi.
“Ƙungiyoyin sun fara da cewa kada a kori kowa, amma daga baya an ce sun amince da 800. Ma’aikatan da abin ya shafa sun kamata su fara karɓar takardunsu daga ranar Litinin, amma an jinkirta, sai jiya aka fara ba su takarda,” wata majiya ta bayyana.
Wata takardar sallama mai taken “Sanarwar Sallama Daga Aiki”, da aka rubuta a ranar 5 ga Nuwamba, 2025, kuma Adeniyi Adejola, Babban Jami’in Kula da Ma’aikata na kamfanin, ya sanya wa hannu, ta tabbatar da cewa aikin na daga cikin “shirin daidaita ma’aikata da ake ci gaba da aiwatarwa.”
Takardar ta kuma bayyana cewa duk ma’aikatan da abin ya shafa za su karɓi haƙƙinsu bayan kammala tsarin sallamar su.
Wani ɓangare na takardar ya ce: “Muna bakin cikin sanar da kai cewa ba za a sake buƙatar ayyukanka a kamfanin nan ba daga ranar 5 ga watan Nuwamba, 2025. Wannan shawara ta biyo bayan sakamakon aikin daidaita ma’aikata da kamfanin ke aiwatarwa. Ka tabbata cewa an yanke wannan shawara bayan dogon nazari da kuma bisa ka’idojin kamfanin.”
“Ana buƙatar ka kammala tsarin sallama a wurin aikinka, ka kuma dawo da duk wani kayan kamfani da ke hannunka kafin ka mika kanka ga wakilin kula da ma’aikata. Kammala waɗannan matakai ne zai ba da damar sarrafa kuɗin sallamarka,” in ji takardar sallamar.