Dangane da fargaba game da karancin abinci na amfanin gona da aka canza jinsinsu (GMOs), farfesan ya ce domin tabbatar da lafiyar abinci da kare lafiyar jama’a, dole ne kowace iri da za ta shigo kasar ta bi matakan doka da ka’idoji da ke tabbatar da cewa tana da aminci. Ya ce, dokokin da ake amfani da su wajen kula da GMOs ma sun fi tsauri fiye da na amfanin gona na gargajiya saboda an kara musu sinadaran halittu (genetic materials).

“Kafin a saki kowane irin amfanin gona domin a fara amfani da shi a kasuwanci, dole ne ta bi diddigin binciken halittu da sinadaran gina jiki sosai. Bayanai da ake da su a halin yanzu sun nuna cewa amfanin gona na GMO suna da lafiya, bisa sama da bincike 200 da aka gudanar a Turai, Amurka, Latin Amurka da wasu kasashen Afirka.

Shi ya sa aka amince a ci su, domin sun cika sharudan tsaro. Babu wani rahoto daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ko kuma Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) da ya nuna cewa amfanin gona ko abincin da aka sarrafa ta hanyar ilmin kwayoyin halitta (GMO) na da illa ga mutane ko dabbobi.

A halin yanzu akwai amfanin gona irin su masara, tumatir, shinkafa, waken suya da gwanda da aka sarrafa ta hanyar GMO a kasuwa. Babu wani tabbacin matsalar tsaro game da hakan.”

Adamu ya ce Nijeriya ba ta samar da isasshen abinci na gargajiya (organic) ba, sai dai amfanin gona na yau da kullum kamar sauran kasashe masu tasowa, inda manoma ke amfani da takin zamani, magungunan kashe kwari da sauran sinadarai.

Ya bayyana cewa amfanin gona na kwayoyin halitta (GM crops), an noman wasu daga cikinsu ne domin su iya jure matsalolin da manoma ke fuskanta a lokacin noman su, kamar kwari masu lalata shuka, irin su stem borer da kuma kwaron fall armyworm.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026 November 7, 2025 Tattalin Arziki Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho November 7, 2025 Tattalin Arziki Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria October 25, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Zulum ya bai wa hukumomin tsaro kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Borno

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa hukumomin tsaro da rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Maiduguri.

Daga cikin motocin, an bai wa rundunar CJTF guda 30, jami’an tsaro 16, ƙungiyoyin tsaro 10, mafarauta shida, sannan aka bai wa hukumar NAPTIP guda ɗaya.

Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka

An raba motocin ne domin inganta sintiri da kai ɗaukin gaggawa, domin yaƙi da laifuka da barazanar tsaro irin su ’yan daba da sauran masu aikata laifi a Maiduguri da kewaye.

Wannan na cikin irin tallafin da Gwamna Zulum ke bayarwa don inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Yayin ƙaddamar da rabon, Gwamna Zulum ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Ya ce: “Gwamnatinmu za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro dukkanin goyon bayan da ake buƙata don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Borno.”

Zulum ya kuma gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da dukkanin jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na wanzar zaman lafiya a jihar.

Taron rabon ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Dakta Umar Usman Kadafur, Sakataren Gwamnati Bukar Tijani.

Sauran sun haɗa da Kwamishinan ’Yan Sanda, Naziru Abdulmajid, Daraktan Hukumar Tsaro, Adamu Umar da sauransu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon
  • Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump
  • Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 
  • Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
  • Zulum ya bai wa hukumomin tsaro kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Borno
  • Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU
  • Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar
  • Dalilin da Trump ya yi iƙirarin ana kisan Kiristoci a Nijeriya — Ndume
  • KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICEF