WFP: Ana Fama Da Matsananciyar Yunwa A Gabashin DRC
Published: 9th, November 2025 GMT
Shirin Majalisar Dinkin Duniya Na Samar Da Abinci ( WFP) ya fitar da gargadi akan cewa, yankin gabashin DRC yana fama da matsananciyar yunwa.
Daraktar cibiyar ta WFP a kasar ta DRC Cynthia Jones ce ta yi wannan gargadin yana mai kara da cewa; Da akwai iyalan da suke tsallaken cin abinci, bayan da su ka sayar da kayan gidansu da kuma dabbobin da su ka mallaka.
Hukumar da yake kula da wadatar abinci ( IPC) ta ce da akwai mutanen da adadinsu ya kai miliyan 25 da suke cikin matakin karshe na yunwa, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3 da suke cikin hatsari.
Hukumar ta MDD ta kuma ce, a halin yanzu mutane suna ta mutuwa saboda babu abinda za su ci a gabashin DRC.
Karancin Abincin da yankin na gabashin DRC yake fama da shi, yana da alaka da fadan da ake yi a tsakanin ‘yan tawayen M23 da sojojin gwamnati a yankin. Gwamnatin DRC dai tana tuhumar Rwanda da cewa ita ce mai goyon bayan kungiyar ‘yan tawayen ta M23 da makamai da kuma sojoji.
Gwamnatin Kigali dai ta sha karyata wannan zargin da ake yi mata.
A sanadiyyar rikicin yankin, mutane miliyan 5. 2 su ka bar gidajensu,a cikinsu da akwai mutane miliyan 1.6 a cikin wannan shekarar kadai.
Cibiyar ta ( WFP ) ta yi kiran gaggawa ga duniya da a kai dauki ga mutanen wannan yankin na gabashin DRC.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa kasuwanci da tsaro November 9, 2025 Tanzania: ‘Yan sanda sun kama wani babban jigon adawar siyasa November 9, 2025 Martanin Iran ya haddasa wa Isra’ila hasarar fiye da Dala Miliyan 200 November 9, 2025 Biden Ya Caccaki Trump Bisa Tuhumarsa Da Kawo Barna November 9, 2025 Masar da Rasha sun tattauna batutuwan tsagaita wuta a Gaza da kuma Sudan November 9, 2025 Dan Wasan Taekwando Na Kasar Iran Abulfazl Zandi Ya Zamo Shi Ne Na Daya A Duniya November 8, 2025 Iraki Na Samun Zaman Lafiya Kuma Tana Kokarin Kawo Karshen Zaman Sojojin Ketare A Kasar November 8, 2025 Turkiya Ta Fitar Da Sammacin Kama Natanyaho Da Wasu Jami’ian Isra’ila Kan Yakin Gaza November 8, 2025 Shugaban Najeriya da takwaransa na kasar Saliyo Sun yi Ganawar Sirri a birnin Abuja November 8, 2025 Nigeria: Za A Ci Gaba Da Zaman Shari’ar Shugaban Kungiyar “IPOB” A ranar 20 Ga Watan Nan Na Nuwamba November 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da sauran ƙasashen duniya “ta hanyar difilomasiyya” game da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a yanzu.
Kalaman shugaban na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar kutsawa Najeriyar domin kai wa ‘yan bindiga hare-hare bayan ya zargin gwamnatin Tinubu da ƙyale su suna “yi wa Kiristoci kisan gilla”
Da yake magana yayin zaman majalisar ministocinsa a jiya Alhamis, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo karshen”ta’addanci”.
“Duk da kalubalen irin na siyasa da fargabar da mutanenmu ke ciki, muna ci gaba da tattaunawa da kawayenmu, muna tattaunawa a difilomasiyyance,”
“Ina tabbatar muku cewa za mu kawo karshen ta’addanci. Abin da muka saka a gaba shi ne cigaba da ayyuka ido bude bisa manufarmu ta Sabunta Fata [Renewed Hope] domin gina Najeriya mai yalwa.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon November 6, 2025 Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki November 6, 2025 Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi November 6, 2025 Putin : zamu dauki mataki idan Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya November 6, 2025 Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Gwamnonin IAEA November 6, 2025 Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho November 6, 2025 Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci