Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla.

A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin wani gida, suna harbi a sama, sannan suka tafi da wasu daga cikin mazauna gidan.

Daga nan ne rundunar ’yan sanda tare da ’yan banga da masu farauta suka isa yankin cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga ceto sun hada da Fatima Wasiu da Kudus Wasiu da jaririya mai watanni shida, ba tare da jin rauni ba.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da nemo sauran mutane biyu da aka yi garkuwa da su, wato Wasiu Salihu da Abdullahi Sefiu, kuma ana ci gaba da farautar wadanda suka aikata laifin.

Rundunar ta bukaci jama’a da su ci gaba da ba da bayanai cikin lokaci, domin sauƙaƙa aikin tabbatar da tsaro a jihar.

Ali Muhammad Rabiu/Kwara

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwara Ceto

এছাড়াও পড়ুন:

Iran : Jagora ya gindaya wasu sharudda kafin yin duk wata hulda da Amurka   

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington ya samo asali ne daga muradun jama’a, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa da Amurka za a iya cimma shi ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta kuma janye dukkan sansanonin sojinta daga yankin, sannan ta daina tsoma baki a harkokin Iran.

Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana hakan yayin ganawa da wani rukunin dalibai na kasar a jajibirin Ranar Dalibai ta Kasa wacce kuma ta yi daidai da ranar kasa ta yaki da girman kai na duniya.

Jagoran ya bayyana ranar a matsayin “ta tarihi” kuma wani muhimmin bangare na asalin Juyin Juya Halin Musulunci.

“Cece-cen da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka abu ne na zahiri, kuma ya samo asali ne daga rikicin muradun dake tsakanin bangarori biyu,” in ji Ayatollah Khamenei.

Jagoran ya bayyana farmakin da aka kai ofishin jakadancin Amurka a shekarar 1979 a matsayin “ranar alfahari da nasara” ga al’ummar Iran.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Musulmi : Falasdinawa ne kadai ke da hakkin jagorantar yankinsu November 4, 2025 Tanzaniya: An rantsar da shugaba Samia a wa’adi na biyu na shugabanci November 4, 2025 Iraniyawa na bikin tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a Tehran a 1979 November 4, 2025 ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam November 4, 2025 Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda  Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Ga Wani Dan Majalisa A Jihar Niger
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara
  • Iran : Jagora ya gindaya wasu sharudda kafin yin duk wata hulda da Amurka   
  • Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha
  • An kashe ’yan bindiga 19 yayin daƙile wani hari a Kano
  • ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka