Leadership News Hausa:
2025-11-08@17:29:28 GMT

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Published: 8th, November 2025 GMT

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

 

Sunana Abdulhamid Ado (Danbayaro):

Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya boye wa mutum gaskiya, kuma baya cin hakkin mutum, kuma abun hannusa baya rufe masa ido.

Kuma indai ya samu abun duniya ko baka sani ba sai ya kira ka an ci da kai, harkar sa ba bakin ciki yana da hali mai kyan gaske. Wata rigar san yi da ya kawo mana ‘location’ ya raba mana dukkan ‘crew’ sai da ya bamu, ina ganin rigar yake fado min tun da ya fara jinya har zuwa yanzun nan da kuma sauran abun alkairai da yayi mana muna tare. Mun yi rashi matuka da gaske, Allah yayi masa rahama, Allah ya kula da bayan sa.

 

Sunana Sarah Aloysius (Edecutibe Producer, Dadin Kowa):

Gaskiya Mun yi babban rashi, ba Dadin kowa kadai ba, Kannywood bakidaya. Malam Nata’ala yana daya daga cikin jigajigan jaruman da masana’antar kannywood ta dogara dasu da fuskar rike aikinsu da muhimmanci. Yana da hakuri da juriya wajen aiki, yana da girmama mutane komai girma ko kankantar mutum, yana da kyauta, abun hannunsa baya rufe masa ido. Malam Nata’ala yana da rike alkawari sosai, ga kyakkawar mu’amala da mutane da kuma barkwanci. Akwai wani lokaci da muka samu matsalar ‘schedule’ na aikin shirin Dadin Kowa, muka kira shi cikin dare cewa, za mu yi aiki da shi washegari, a lokacin bai ma fada mana baya kasar ba, amma haka muka tarar da shi washegari a ‘location’. Haka kuma a lokuta da dama, sai ka ganshi ya zo ‘location’ da kayan tsaraba ya rabawa ‘crew members’. Kawai sai dai muce Allah yayi masa rahma, ya haskaka kabarinsa.

 

Sunana Fati Al’amin wacce aka fi sani da Maman Badaru:

Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un, wallahi na girgiza da jin rasuwar Malam Nata’ala sosai. Hakika mun yi babban rashin mutumin kirki wanda abin duniya bai rufe masa ido ba. A duk lokacin da muka fita wajan wani aiki ko wata gaiyata da aka yi mana wallahi shi ne yake shugabantar tafiyar. Amma abin da zai baki sha’awa da rayuwarsa duk wani alkhairi da aka samo to, fa baya bari a wajansa. Ni yake bawa ya ce, na ajjiye har sai mungama samun abin da aka bamu, sannan ya ce Fati na yarda da amanarki ki raba ki bawa kowa hakkinsa [Kuka]. Ni kuma sai na raba na bawa kowa, sannan na fitar masa da na sa dan shi ne ya kawo harkar. Wani lokacin har nakan yi bakin jini a wajan wasu su ce na cika masa, ni kuma sai na ce da bai kawo aikin ba fa?. Allah ya ji kansa da rahma ya sa aljanna makomar sa. Wallahi ina tuna shi ta son kawo wa al’umma alkhairi, ba tare da bakin ciki ba, ga son ciyarwa ga al’umma, Allah yayi masa rahma.

 

Sunana Alh. Dauda Adakawa, wanda aka fi sani da Malam Barau na Dadin Kowa:

Rasuwar malam Nata’ala ta girgiza ni da kyau, kasancewar ni ne kamar sa’ansa kuma aboki wanda ko harkar rashin lafiyarsa, da ni muke yawan magana da yan’uwansa, musamman Sadi Potiskum. Malam yana da karamci, jin kai, da son abokan aikin sa, sannan mai son kowa ya samu alkhairi ne. Gaskiya akwai abubuwan da za mu kare rayuwar mu muna tuna Malam Nata’ala da shi, kamar; Kyauta, gaskiya, da son jama’a.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nishadi Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar November 1, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales October 25, 2025 Nishadi Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad  October 11, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna tsoron wanda zai yi tunani a gaba, saboda duk wanda ya kawo wani ilimi sai ka ji an ce Zindiki ne, sai a so a halaka shi ma idan ba a yi wasa ba. Toh abin da ya dinga faruwa kenan har Allah Ya kawo falasfawa na Greeks Socrate, wasu sun ce Annabi ne, suka zo suka canza ilimi shi kan shi wannan Socrate din kashe shi aka yi da aka ce ko ya ce bai yarda da wannan ilimi ba, ko ya sha dafi shi kuma ya ce Allah ba zai ba shi ilmi ba, don haka gwara ya sha dafi ya mutu ya yarda ya sha, ga shi su wanda suka kashe shi ba sunansu shi kuwa har yau sunansa a duniyar ilimi ba zai bace ba. Toh Allah kuma Ya kawo juyin juya hali daga karni na 1800 har ya zuwa 1900 ilimin ya soma yalwata da aka fara rubuta shi, wasu na cewa ba mahaukaci sai wanda ya ba da aron littafi, ba wanda ya fi shi hauka sai wanda ya dawo da shi, wannan a lokacin da ake rubuta littafi da hannu kenan amma yanzu ya kare, an ce Shehu ya zo gidan daya daga cikin shehunnanmu yana duba library sai ya ga wani littafi sai ya ce ka ga wannan littafi na neme shi ban samu ba, ba ni aro sai ya ce Shehu na ba ka aro dauki, sai Shehu ya ce masu hikima sun ce babu mahaukaci sai wanda ya ba da aron littafi, ba wanda ya fi hauka sai wanda ya dawo da littafi, ya ce ni dai ba zan zama mahaukaci ba, sai Shehu ya yi masa wasa.

To da aka soma rubutun, China kamar su suka soma, to da buga littafi ilimi ya soma ya]uwa zuwa ga jama’a, ilimi ya fito daga dakin bauta, ya fito daga masarautar sarakuna ya shiga gidan kowa, a da kuwa yana gidan sarakuna ne kawai, ilimi ya soma yaduwa har Allah ya kawo Rediy,o tana daga cikin abin da ya yada ilimi, ta yi hobbasa wajen wayar da kan komai, dan haka a kula da rediyo yana da matukar kyau saboda galibin mutane rediyon nan ita ce hanyar daukar maganarsu, Allah ya saka wa Shehu Ibrahim Inyass (RA) da alkhairi, ya sha wahala wajen sa karatun Kurani a ciki, har Allah ya kawo talabijin, har “cable” din nan ta zo, yanzu fa za ka iya ganin duniya a cikin abu, karshen wayewa, karshen ci gaba a yanzu kuma wayar salula, wadannan wayoyi da suke hannunmu sun sa a yanzu babu jahili sai dai dakiki wanda ya ki sani da gangan, amma wayar nan babbar farfesa ce ta kowane karni, idan fannin jinya ne za ta fada ma har abin da hankalinka ba zai taba kawowa ba, haka a fannin alheri, idan fannin tarihi ne za ta kai ka har inda kudinka ba zai iya kai ka ba. Alhamdu Lillah, mun gode Allah.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Dausayin Musulunci Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya October 17, 2025 Dausayin Musulunci Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2) October 10, 2025 Dausayin Musulunci Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi October 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa
  • Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura
  • GORON JUMA’A
  • Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon
  • An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
  • Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah
  • Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
  • Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu