Aminiya:
2025-11-05@21:19:38 GMT

Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu

Published: 5th, November 2025 GMT

Majalisar Dattawa ta dakatar da aikin tantance Dokta Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa domin zama minista, sakamakon rashin gabatar mata da rahoton jami’an tsaro a kansa.

Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce ba za su ci gaba da tantancewar ba sai an samu cikakken rahoto daga hukumomin tsaro.

Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano

A ranar Talata ce Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar sunan Mista Udeh, ɗan asalin Jihar Enugu cikin wata wasiƙar neman sahalewarta.

“Ina farin cikin miƙa sunan Dokta Kingsley Tochukwu Ude, SAN, domin tabbatar da shi a matsayin minista. Ina fatan majalisar za ta yi la’akari da wannan buƙata cikin gaggawa kamar yadda aka saba,” in ji wasiƙar shugaban ƙasan.

Tinubu ya naɗa Udeh ne bayan murabus ɗin da tsohon Ministan Kimiyya, Uche Nnaji ya yi, bayan zargin da aka yi masa na gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta bogi, wanda kuma shi ne minista ɗaya kacal daga Jihar ta Enugu

Mista Udeh wanda yanzu haka shi ne Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Enugu, ya shahara da ƙwarewa a fannin doka da kare haƙƙin ɗan Adam.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Dattawa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

 

Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista November 5, 2025 Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio November 5, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai
  • Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 
  • Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio
  • Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150
  • An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump
  • Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani
  • Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya
  • ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu
  • Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha