Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza
Published: 7th, November 2025 GMT
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a kafa kwamitin kasa da kasa domin tantance makomar wadanda suka bata a Gaza
Shugaban Kwamitin Binciken Mutane da Suka Bace a tawagar Babban Hafsan Rundunar Sojin Iran, Birgediya Janar Seyyed Mohammad Baqirzadeh, ya gabatar da shawarar kafa kwamitin kasa da kasa don neman fiye shahidai 10,000 da suka bace a yankin Gaza.
Birgediya Janar Baqirzadeh ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na bangarori uku wanda ya hada da Iran, Iraki, da Kwamitin Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), da nufin tantance makomar shahidai da suka bace da kuma mayar da gawarwakinsu ga iyalansu. Ya jaddada muhimmancin rawar da Kungiyar Red Cross take takawa wajen bin wannan batu na jin kai.
Birgediya Janar Baqirzadeh ya kuma ba da shawarar a bi diddigin mayar da gawar shugaban kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da ya yi shahada Yahya Sinwar ga iyalansa a Gaza, domin dawo da martabar shahidai.
Zirin Gaza ya sha fama da kisan gilla da ake a cikinsa tsawon shekaru, wanda ya haifar da dubban shahidai da mutanen da suka bace, ciki har da fararen hula marasa laifi, mata, da yara, wanda ya bar makomar mutane masu yawa ba a sani ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Babban Matsalar Jin Kai A Falasdinu, Inda Falasdinawa Miliyan 1.5 Suke Cikin Halin Bala’i November 7, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya November 7, 2025 Karuwar Matsalar Jin Kai Mafi Girma A Duniya A Sudan Saboda Ci Gaba Da Masifar Yaki A Kasar November 7, 2025 An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jinin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari
Iran ta sanar da yi wa ‘yan faransa nan guda biyu da take tsare saki bisa sharadi a zarginsu da akeyia da yi wa tsaron kasar Iran zagon kasa.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya fitar da bayanin sakin yana mai cewa na yi shi ne “bisa umarnin alkali.”
Ya kara da cewa za su ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar shari’a har sai an ci gaba da shari’a.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana mutanen biyu a matsayin Cécile Kohler da Jacques Paris, wadanda aka tsare a Iran bisa zargin leken asiri.
A halin yanzu suna Ofishin Jakadancin Faransa da ke Tehran.
A ranar 21 ga Oktoba, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Vahid Jalalzadeh ya sanar da cewa Mahdieh Esfandiari, wata ‘yar Iran da aka tsare ba bisa ka’ida ba a Faransa saboda wallafa sakon goyan bayan falasdinu a kafofin sada zumunta, an saka ta cikin shirin musayar fursunoni.
A ranar 22 ga Oktoba, Mista Baghai ya sanar da sakin Ms. Esfandiari bisa sharadi a cen faransa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Karon farko an zabi Musulmi magajin New York, birni mafi girma a Amurka November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci