Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila.

Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan  ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da suke buga gasar Premier League ta bana.

Ƙungiyoyin da suka ci riba;

LIVERPOOL

Ƙungiyar ce kan gaba a yawan kashe kuɗi wajen sayen ƴan  ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan  wasa a matakin mafi tsada a kakar nan. Ta fara da sayen matashin ɗan wasa Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Aleɗander Isak kan fam miliyan 125 ranar da za a rufe kasuwar.

Cikin ƴan  ƙwallon da ta saye har da Jeremie Frimpong kan fam miliyan 30 da Milos Kerkez kan fam miliyan 40 sai kuma Hugo Eketike, ɗan Faransa, wanda ya koma ƙungiyar dafa Frankfurt. Haka kuma Liɓerpool ta sayer da Luis Diaz da Darwin Nunez da Jarell Ƙuansah daga ƙarshe ba ta samu damar sayen Marc Guehi daga Crystal Palace ba, bayan da Palace ɗin ta ce ba ta samu ɗaukar madadin Guehi ba.

ARSENAL

Arsenal ta fitar da maƙudan kuɗaɗe wajen sayen ƴan  wasa da yawa, domin taimakawa Mikel Arteta a ƙoƙarin da yake na ganin ya lashe kofuna a bana, musamman Premier League, wadda rabonta da kofin kaka 22 kenan. Cikin ƴan  wasan da ta ɗauka har da Viktor Gyokeres, wanda ya kawo matsalar rashin mai buga gurbin cin ƙwallaye, bayan da ke fama da jinya.

Haka kuma Arsenal ta sayi Eberechi Eze da Noni Madueke da Martin Zubimendi da Christian Norgaard da Cristhian Mosƙuera da kuma Piero Hincapie. Bugu da ƙari ƙungiyar ta London ta ɗauki mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga, duk dai domin ta taka rawar gani a kakar nan, sannan Arteta ya ƙara lashe kofuna bayan FA Cup a kakarsa ta farko da kuma Community Shield.

NOTTINGHAM FOREST

Tuni ƙungiyar ta kori kocinta, Nuno Espirito Santo bayan rashin fahimtar juna da suke ci gaba da samu da daraktan ƙwallon ƙafa na  ƙungiyar, Edu Gaspar, Forest ta shiga kasuwa ta yi cefanen ƴan  wasa don ganin ta yi abin kirki a kakar nan.

Sau biyu a ƙungiyar tana sayen ɗan wasa a matakin mafi tsada a tarhinta, bayan sayen Dan Ndoye da kuma Omari Hutchinson. Sannan ta kuma kashe fam miliyan 30 kuɗin sayen James McAtee, sai kuma Douglas Luiz da ya koma buga Premier League daga Juɓentus ta kuma ɗauki Nicolo Saɓona.

A ranar da za a rufe kasuwar cinikin ƴan  ƙwallo ƙungiyar ta sake ɗaukar aron Oleksandr Zinchenko ta sayi Dilane Bakwa, sannan ta kuma yi nasarar riƙe ɗan wasan tawagar Ingila, Morgan Gibbs-White, bayan da Tottenham ta yi ƙoƙarin sayen ɗan ƙwallon.

Sai dai duk da haka akwai ƙungiyoyin da za a iya cewa asara suka yi a wannan kakar idan aka kalli yan wasan da suka sayer da kuma waɗanda suka saye kafin a rufe kasuwar

NEWCASTLE UNITED

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle United ta sayi ɗan wasan Brentford, Yoane Wissa da ɗan ƙwallon Stuttgart, Nick Woltemade, wadda ta fara da ɗaukar ɗan wasan Nottingham Forest, Anthony Elanga.

Sai dai kuma ba za a manta da batun Aleɗander Isak ba, wanda ya dage sai da ya bar ƙungiyar, har da ƙin buga mata wasannin atisayen tunkarar kakar bana da wasa biyu da ta buga a Premier League ta bana.

Kuma rashin Isak ya sa tana shan wahala wajen cin ƙwallaye, hakan ya sa ta yi zawarcin madadinsa daga ciki har da Hugo Ekitike da ya zaɓi Liɓerpool da Benjamin Sesko da ya koma Manchester United har da Joao Pedro da ya zaɓi Chelsea sai  kuma Jorgen Strand Larsen, wanda Woɓes ta ƙi sayer da shi.

ASTON VILLA

Ita ma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa tana fatan yin gogayya cikin ƴan  shidan farko a Premier League a kakar nan, amma ta ci karo da cikas kan dokar kashe kuɗi daidai samu. Duk da haka ta sayer da matashi, Jacob Ramsey, wanda magoya baya ba su ji daɗi ba.

Sai dai ƙungiyar ta ɗauki Harɓey Elliott daga Liɓerpool da kuma ɗan wasan Manchester United, Jadon Sancho, amma dai Villa ba ta samu yin cinikin da zai bata damar yin abin kirki ba, kenan sai abin da ta gani.

BRENTFORD

Bayan da Brentford ta rasa kociyanta, Thomas Frank da ya koma Tottenham ta kuma sayer da ƴan  ƙwallo uku da ya haɗa da Bryan Mbeumo ga Manchester United, yayin da Norgaard ya koma Arsenal da kuma Newcastle da ta sayi Wissa. Sai dai ta sayo Dango Outtara daga Bournemouth kan fam miliyan 42.5, amma dai tana da jan aiki bayan rashin fitattun ƴan  ƙwallonta uku a kakar nan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yan Wasa Firimiya Transfer kan fam miliyan ƙungiyar ta a kakar nan

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025

Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.

Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.

Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.

Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha
  • Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff
  • Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana