Aminiya:
2025-11-18@11:02:30 GMT

Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico

Published: 2nd, October 2025 GMT

Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200.

Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Babban malamin Qur’ani da ƙira’a na Masallacin Madinah ya rasu

Kocin Atletico, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa kan ƙwazon ɗan wasan, inda yake cewa “ba ruwan hazaƙa da shekaru.

Griezmann mai shekaru 34, ya kwashe kusan shekaru 10 a Atletico kafin ya cim ma wannan mataki.

A cewar Simeone, “ina godiya ga Antoine da lokacin da ya kwashe a Atletico Madrid. Ya ci ƙwallo 200, wanda abin al’ajabi ne.”

A ƙarshen kakar bara, an yi ta raɗe-raɗin Antoine Griezmann zai bar ƙungiyar, amma sai ya tsawaita kwantiraginsa zuwa 2027.

Sai dai a kakar bana, mintuna 416 kawai ya buga zuwa yanzu a wasanni tara, inda yake yawan shigowa wasa daga benci.

A halin yanzu, a kakar bana ana hasashen Griezmann zai zama ɗan Atletico na huɗu da ya buga mata wasanni 500, bayan Adelardo, da Koke, da kuma Jan Oblak.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanzu-yanzu: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP
  • Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi
  • Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi
  • Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
  • Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi