Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato
Published: 8th, November 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga da Bello Turji ke jagoranta sun kai hari ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato da safiyar ranar Asabar.
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe mutum biyar, tare da jikkata wani ɗan sa-kai, sannan suka sace wasu mutum tara waɗanda mafi yawansu mata ne.
Kafin faruwar harin, wani mai ɗan gwagwarmaya a yankin mai suna Basharu Altine Guyawa, ya wallafa a kafafen sada zumunta inda ya yi gargaɗin cewa Bello Turji da tawagarsa suna shawagi a yankin Fadanar Tursa da Dorawar Madugu zuwa Dan Huntuwa ta gadar Katutu, wacce ta haɗa ƙananan hukumomin Shinkafi da Isa.
Guyawa, ya bayyana cewa Turji tafe da maharansa a kan babura 40.
Haka kuma ya zargi hukumomin yankin da jami’an tsaro da rashin ɗaukar mataki duk da samun wannan bayanai.
Amma Shugaban Ƙaramar Hukumar Isa, Alhaji Sharehu Abubakar Kamarawa, ya ƙaryata zargin.
Ya ce tun bayan samun bayanin, suka tura jami’an tsaro domin ɗaukar matakin.
“An tura jami’an tsaro zuwa wajen da aka samu labari, amma daga baya bayanan sirri suka nuna cewa ‘yan bindigar sun bi wata sabuwar hanya, abin da ya haifar da wannan mummunan hari,” in ji Kamarawa.
Ya ƙara da cewa an sauya kwamandan tsaron yankin bayan binciken da aka gudanar tare da gano matsaloli wajen tsara aikinsa.
Kamarawa, ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa tare da tabbatar cewa gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Hakazalika, ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu bisa ƙoƙarinsa na yaƙi da ta’addanci, musamman ta hanyar raba motocin sintiri da babura ga jami’an tsaro ba su alawus na wata-wata.
Duk da waɗannan ƙoƙari, matsalar rashin tsaro na ci gaba da addabar wasu sassan Jihar Sakkwato, musamman yankin gabas, inda ’yan bindiga ke ci gaba kai wa yankunan karkara hare-hare.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari Sakkwato yara jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti
Kwamandan Ƙungiyar sa kai ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) reshen Jihar Kaduna, Abdulwahab Muhammed ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta amince da Ƙungiyar a matakin ƙasa ta hanyar sanya hannu a kan ƙudurin da aka gabatar.
A cewar ƙungiyar bisa la’akari da irin rawar da take takawa wajen daƙile ayyukan miyagu da samar da tsaro a sassan ƙasar nan.
An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawaYa ce lokaci ya yi da gwamnati za ta sa hannu kan kudurin amincewa da kungiyar domin kasancewa cikin jerin hukumomin tsaro na kasa, la’akari da irin jajircewar da suke nunawa musamman a Jihar Kaduna.
Abdulwahab ya bayyana hakan ne yayin taron ƙarin girma da ƙungiyar ta shirya ga wasu jami’anta a Ƙaramar hukumar Jama’a, inda kuma aka karrama wasu fitattun mutane da ke ba da gudunmawa wajen tallafa wa ayyukan tsaro.
Kwamandan ya ce, suna da kyakkyawar fahimta da haɗin kai da sauran jami’an tsaro, inda suke miƙa waɗanda suka kama ga ’yan sanda don gudanar da bincike da yin hukunci bisa doka. Ya roƙi gwamnatin jihar Kaduna da ta ƙara tallafa musu da kayan aiki domin sauƙaƙa gudanar da ayyukansu.
Shi ma Shugaban karamar hukumar Jama’a Peter Tanko Dogara wanda sakataren Ƙaramar hukumar Jama’a, Dakta Shehu Usman Danbala ya wakilta, ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar wajen tabbatar da tsaro a matakin sa kai, tare da kiran al’umma da su riƙa basu cikakken goyon baya.